Mafiya yawan lokuta mutane kan siyi shirt coins ne saboda ganin gara ba sar sa, ko kuma saboda son banza. Domin da abinda bai kai $10 ba mutum zai Iya mallakar tiriliyoyi na wannan silallan, hakan shine yake rudar mutane da yawa, domin wai a irin tunaninsu shine, wadannan sulallar ko da ace darajar su kobo kawai takai tofa su sunyi fita da fitarsu. Ga duk mai irin wannan tunanin to tabbas ta tabbata gareshi baisan harkar kasuwancin Crypto ba, abunda ya kamace shi shine ya dannan wannan rubutun domin ganin matakan da yakamata ace mutum yabi yayin fara ko wane irin kasuwanci, bama wai na online ba.
Inda ace
mutane sun san menene shirt coins, sun kuma San tsarinsa, to da dayawa daga
cikin mutane baza susa ko da kwandalace ba wajen siyan wadannan silallan, bare
kuma har susa wasu daloli kuma harma su sa ran cewa wani zai basu kudi a kas.
Bamuce dukkan nin shirt coins ne suka taru suka zama daya ba, amman mafi yawa
daga cikin su shirmene da kuma yaudara. Nasan dayawa daga cikin mutane ba
lallaine su gaskata wannan maganar tawaba, amman ina fatan izuwa karshen wannan
bayanin nawa su samu hujjojin da zasu Iya sa su, su dan gamsu ko dan yayane, ba
dan komai ba sai dan susan inda yakamata ace suringa sa kudaden su yayin
kasuwancin silallan yanar gizo-gizo (Crypto currency).
Shirt coins
ba komai bane ba illa bace wadannan sababbin silallan ne da ake ta kirkirar su
a Crypto a duk kwanan duniya, wanda da kudi dan kadan zaka Iya mallakar miliyoyi
ko biliyoyin wadannan silallan. Sau da dama idan muka kalli yadda tsarin shirt
coin yake, mukan ga yana yi mana kama da caca, domin caca ce kawai ke da wannan
siffar da zan sa kudi kai ma kasa sannan wani daban ya kwashesu, ya barmu da
lahaula kawai. Watakila in mukaga yadda tsarin shirt coin yake tafiya za mufi
gamsuwa d wannan bayanin nawa.
Sanin
kanmune da cewa duk wani coin da aka kirkira akwai abunda ake alakantashi da
shi wata case use dinsa kenan, wannan case use din nasa shine zai bawa mutane
dama suringa siyansa domin amfanin Kansu. Misali, idan mukai duba da bitcoin
(BTC) zamuga babban dalilin da yasa aka kirkireshi shine, saukaka wa al'umma
wajen kulla kasuwancin su a sassan duniya daban-daban. Domin samun cikakken
bayani akan hakan, maza danna wannan rubutun Dan ganin cikakken bayanin.
Bayan case
use, akwai abunda muke kira d user ability. Abunda ake nufi da user ability
anan shine, idan har an alaqanta coin da wata matsalar mutane, to wace hanya
ake da ita da zata sa mutane sukarbi wannan coin din domin kawarwa da Kansu
wannan matsalar. Allal misali, idan yazamana cewa yau an kirkiro wani Sabon
Coin, sai akace dalilin siyansa shine za aringa shiyan shinkafa da shine. Bil
hakika wannan dalilin mai kyau ne, domin muddin dai jama'a suka yarda dacewa
zasuringa siyan shinkafa da wannan coin din, to babu makawa zaiyi tsada, domin
kuwa kullum sai ansai shinkafa, inkuwa yazamana cewa kullum za'a sai shinkafa,
ya zamana cewa kenan kullum za'a sai wannan coin din, in kuwa kullum za'a sai
wannan coin din, to kuwa babu makawa zai ringa tashi. Amman ba anan gizo yake
sakarba, abun tambaya anan shine, menene tabbacin cewa 'yan kasuwa masu sai da
shinkafa zasu yarda suringa karbar wannan coin din a mai makon Kudin zahiri.
Yau da ace
manyan kamfanunnuwan shinkafa irin su kamfanin dangwate da makamantansu za suce,
duk wanda zai sai shinkafar su da Naira to duk buhu daya za su siyar masa da
shi ne akan naira 100. Idan kuma mutum zai siyane da wannan sabon coin din, to
za su siyar masa akan naira 90. Adalilin wannan rangwamen naira goman, dayawa
daga cikin mutane za su kammaci cewa gwara suringa siya da coin dinnan akan
kudin gaske. Wannan dalilin da yasa mutane suka gammaci suringa siyan shinkar
da coin akan kudin gaske shi muke kira da user ability.
Mutukardai
yazamana cewa 'yan kasuwa zasu ring a karbar wannan coin din amatsayin kudi, to
babu shakka duk Wanda yasai wannan coin din bazai asara ba, domin ko ba dade bo
bajima wannan coin din zaiyi daraja a idan duniya, ba dan komai ba sai dan
kullum sai ansamu masu siyan wannan coin din. Irin wadannan coins din da suke d
user ability muke kira ga mutane suringa rikesu domin cin moriyarsu. Amman in
yakasance cewa coin baya da wani user ability to kuwa tabbas akwai yiwurar dakonsa
mutum kawai zaiyi, domin kuwa babu mai siyan sa barema asa masa ran cewa
watakila zai yi daraja anan gaba.
Ga duk Wanda
yasan tsarin mafi yawancin shirt coin, zaiga cewa basa da wannan user ability
din, kodama ace suna d case use, domin bawai case use dinne mai amfani ba, user
ability din sine mafi amfani, domin shine zai daga darajar wannan coin din
izuwa har illamasha Allah.
Mafiya yawan
lokuta zamuga cewa yawancin shirt coins darajarsu a kasuwa na fara wani irin
mugun tashi, wanda hakan shiyake rudar mutane dayawa su siyi wannan coin din da
zummar wai koda ace sisi ko kwabo yakai sai suyi fita da fitarsu, daga bisani
kuma sai muga wannan coin din yayi muguwar wata karyewa, in ba ai wasaba kuma
shikenan wannan coin din baza a qara jin duriyarsaba, wadanda suka ciriba sunci
riba, wadanda kuma tarutsa dasu aciki shikenan sai dai kuma wani jikon Amman
kudinsu kuwa, ya mula. To wai shin meyasa hakan take kasancewa ne.
Yadda tsarin
yake shine, akwai abunda muke kira da liquidity a turance, wato kudin da za'a
sawa coin yayin da aka kawoshi kasuwa, wadannan kudaden sune idan mutum yakawo
irin wadannan coin din zai siyar za adauka abashi. To duk wani coin din duniya
sai ansa masa wadannan kudaden kafin a iya siyansa ko sai dashi, bacin an sanya
masa wadannan kudaden to duk kuma wanda yazo yakara sa kudi yasai wannan coin
din, to tamkar akan wadancan kudaden ya kara, wato liquidity din coin din. In da
$10 ne liquidity din, sai kazo ka sai na $5, to za'a kara $5 dinnan ta ka akan
waccen $10, kunga kenan yakoma $15. Haka
zalika kuma in siyarwama kai, to a cikin $15 dinnan za adauka a biyaka.
Yadda tsarin
hawa da saukar kowane coin ke kasancewa shine, idan adadin coins din da mutum
ya kirkira wato total supply guda dari ne, kuma yanason ya fito a kan $1 duk
guda daya, to dolene kowane daya daga cikin darinnan yasa masa $1 daya, kunga
kenan in yazamto cewa kowane guda daya daga cikin darin nan zai samasa $1,
kenan jimilla ya kama zai sa $100 akan dukkanninsu. Idan mai coin din yai haka
shine zamuga cewar kowane coin ya fito a dala dai-dai. Duk lokacin da wani kuma
yazo ya sai na $10 to wannan $10 za akaratane akan $100 dinnan, kunga kenan
sabon liquidity na wannan coin din ya koma $110. Tunda kuwa liquidity yaqaru,
dole kuwa farashi zai canza. Taya farashi zai canza, shine zamuce sabon
liquidity a rabashi adadin coins din d suka rage, wannan shine zai bamu sabon
farashin wannan coin din. Kunga kenan zamuce $110÷90 wato adadin coins din, tun
da wan can da yasai Na $10 anbashi guda goma, sabon farashin din coin dinmu zai
kama $1.22, kunga kenan ansamu karin farashi. To haka zalika inda wani zai qara
siyan na $20 farashinmu zai kara canzawa izuwa $1.85. To in kun fahimceni da
kyau, za kufahimci cewa a duk sa'ilin da aka samu wani ya sai wannan coin din
to tabbas farashin wannan coin din sai ya karu, haka zalika da ace wani kuma
zai sai da wannan coin din, to fa babu makawa akancewa farashin wannan coin din
zaiyi kasa.
Idan har
kunfahimci wannan bayanin da kyau, sai muga misalin yadda tsarin kasuwancin
shirt coins yake gudana.
Alal misali
ace, mukirkiri wani coin mai suna a-mangroup coin akalla guda dubu daya,
yazamana cewa wannan coin din namu shirt coin ne, sannan kuma farashin da
mukeso yafito akai shine $1, kunga kenan aqalla muna buqatar musa masa
liquidity din $1000. To bari muga yadda coin din namu zai kasance daga karshe.
|
Name |
Price |
Liquidity |
Buy |
Sell |
New price |
Total |
|
No body |
$1.0 |
$1000 |
No |
No |
$1.0 |
1000 |
|
Nasir |
$200 |
$1200 |
Yes |
No |
$1.50 |
800 |
|
Fatima |
$450 |
$1650 |
Yes |
No |
$3.3 |
500 |
|
Nasir |
$660 |
$990 |
No |
Yes |
$1.41 |
700 |
|
Abdul |
$600 |
$1590 |
Yes |
No |
$5.80 |
274 |
|
Fatima |
$1740 |
-$150 |
No |
Yes |
$0 |
550 |
Idan muka
kalli wannan table din inda mukai bayani a cikin sa, zamuga cewa a mataki na
farko babu Wanda yasai wannan coin din namu, hakan yasa farashin sa bai canzaba
daga $1, wanda kuma liquidity dinsa shima bai wani canzafa domin babu wanda ya
siya bare yasiyar.
Amataki na
biyu zamuga cewa Nasir yasa $200 domin siyan wannan coin din, hakan yasa
liquidity na wannan coin din ya karu da $200, kuma farashin sa ya canza izuwa
$1.5, adadin coin din kuma ya koma 800. Amataki na uku zamuga cewa Fatima $450
inda tasamu damar mallakar wannan coin din namu guda 300, wanda hakan ya bawa
coin dinmu damar kara farashi izuwa $3.3 saboda karuwar liquidity da muka samu
izuwa $1650 bacin fatima ta kara mana $450 na siyayyar da tai mana.
Daman ga duk
Wanda yasan tsarin shirt coin, bawai coin ne da ake holding din sa ba, shiyasa
ake cewa mutane daga zarar sun siya to kada suyi nisa da kasuwa domin dazar
sunga sun danci wata riba, to kawai sufita daga kasuwar. To sai mukaddara cewa
Nasir yasan wannan tsarin. Kai kodama ace bai san hakan ba, mutukar dai yana da
wayo babu yacce za ai ace Kasai shirt coin a $1 kuma wai har ya kai $3.3 kuma
kazuba masa ido kana kallonsa ba. Zamuga cewa idan har Nasir ya dawo da coin
dinnan nasa kasuwa a wannan farashin na $3.3 to fa zai samu $660, wanda hakan
zai haifar da raguwar liquidity dinmu izuwa $990, farashin coin din kuma zai
koma $1.41, adadin coin din kuma zai koma 700 ne.
Amataki nagaba
kuma sai Abdul yasa $600 ya sai adadin coin din nan guda 426, wanda hakan yasa
yawan coin din ya koma 274, liquidity dinsa kuma ya koma $1590 wanda hakan yasa
farashin wannan coin din yakoma $5.80.
A matakin
gaba kuma zamuga cewa Fatima ta dawo da coin din ta kasuwa inda ta sai dashi
akan $1740, Wanda adadin coin dinmu yanxu yakoma 550 kenan, kuma liquidity din
da muke dashi yanxu $-150. To kunga a wannan matakin da muke, babu batun wani
liquidity domin bashima ake bin wadannan masu coin din.
Idan muka
lura da kyau zamuka cewa asannu a hankali ana shiga kasuwar tamu ana fita za
akai matakin da liquidity din coin din namu zai kare, dazarar kuma ya kare
shikenan Babu kuma wani Wanda zai Iya Kara siyansa ko sai dashi. Idan mun
fahimci wannan misalin zamuga cewa a karshe dai Abdul in bai wasaba, shikenan
yayi asarar kudin sa, domin babu liquidity din da za a biyashi kudin sa.
Wani abu da
dayawa daga cikin mutane basu sani ba shine, yawancin masu tallan shirt coin,
da kuma wadanda suka kirkiri coin din macutane, domin kuwa su masu tallan coin
din idan kaduba za kaga kawai kasuwancin su suke bugawa, domin idan har suka
siyarma da coin na $10, to insha maka Allahu da za kai yinkurin sai dashi to
zakaga ashe bai fi na $3-$4 suka baka ba inmafa yakai din kenan. Su kuwa
wadanda suka kirkiri coin din yadda suke nasu zaluncin shine, da fari sukan sa
rabin adadin koyin din da suka kirkira, da zarar sunga mutane sun fara tara
musu liquidity kawai sai su dawo da ragoqar rabin su kwashe kusan dukka
liquidity din da aka tarawa coin. Bamuce dukka aka taru aka zama daya ba, amman
dai mafiya yawansu haka suke.
Wannan kusan
dai shine iya abinda zamu Iya cewa fahimtarmu kenan game da shirt coin, kuma
idan mukai duba na tsanaki zamuga cewa yayi kama da caca kamar dai yadda muka
fada a dazu, domin wasu ne suke kwashe kudin wasu su tafi dashi, kamar dai
yadda Nasir da Fatima suka kwashe kudin Abdul suka tafi dashi. Muna fatan 'yan
uwa da abokan arziki za su fa idantu, su kuma san inda yakamata ace za surinka
saka kudaden su, yayin fara kasuwancin yanar silallan gido-gizo (Crypto
currency). Mungode.
0 Comments