Currencies sune kudaden da kowace kasa take amfani da su yayin kulla kasuwanci. Kamar yadda muka sani cewa kudi duk wani abu ne da mutane suka yadda da shi a matsayin abunda za su ringa amfani da shi a tsakanin su yayin kulla kasuwanci, hakanne yasa ko wace kasa take da irin nata nau'in kudin.
Lokuta mabambanta akan samu kudin wata kasar yafi na wata kasar daraja, wanda hakan yasa idan mutane suka fahimci cewa darajar kudin wata kasar zai tashi sai su mallake shi ta hanyar amfana da ribar sa lokacin da ya tashi din.
Kasuwar forex kasuwace da take bawa mutum damar canza kudin sa izuwa kudin wata kasar, misali, mutum kan iya canza Dallar Amurka izuwa Pound Sterling, ko kuma Euro zuwa Canedian Dollar.
MAJOR CURRENCY DA KUMA MINOR CURRENCY
Major Currency:- major currency sune manyan kudaden da sukafi shahawar da kuma yawan amfani da su a kasuwar forex. Sune kudaden da suka fi bada riba a kasuwar forex, badan komai ba sai dan karbin volatility (yawan siye da siyarwar su) da suke da shi.
Major currencies sune kudaden da ake iya canjar su (Buy) ko canjar da su (Sell) da dalar amurka kawai. Adadin major currencies guda bakwai ne, sune kamar haka:-
- GBPUSD ( Pound Sterling vs US Dollar)
- EURUSD (Euro vs US Dollar)
- USDCHF (US Dollar vs Swiss Franc)
- USDJPY (US Dollar vs Yen)
- AUDUSD (Australian Dollar vs US Dollar)
- NZDUSD (New zealand Dollar vs US Dollar)
- USDCAD (US Dollar vs Canadian Dollar)
Wadannn sune muke kiransu da major currencies, kuma sune kudaden da mutum ya kamata yafi mai da hankali akai yayin yin analysis.
MINOR CURRENCIES:- Bacin major currencies, minor currencies sune ke da daraja ta biyu ta fuskar daraja da kuma kawo ri ba. Idan muka cire Dalar Amurka a cikin major currencies sannan muka hadasu da junansu, shine zasu bamu minor currencies. Misalin minor currencies sune kamar haka:-
- AUDCAD (Australian Dollar vs Canadian Dollar)
- EURJPY (Euro vs Yen)
- EURGBP (Euro vs Pound Sterling)
Wadannan sune kadan daga cikin misalan minor currencies, wanda karfinsu baikai kamar na major currencies ba.
Domin Karin bayani Ku kalli wannan video
Bacin major currencies da minor currencies akwai wasu currencies din, sai dai su karfin su da kuma tasirin su bai kai na major da minor currencies ba, wanda a shawarce muna bawa mutane shawarar da su takaita kawai akan major da minor currencies yayin yin trading din amatakin farko.
Wannan dan takaitaccen bayani ne a game da major currencies da kuma minor currencies kenan, muna fatan 'yan uwa sun dan amfana da wannan dan ta kaitaccen bayanin namu. Arubutunmu nagaba zamu zo muku da bayani akan Base currency da Quote currency, Spread da kuma bayani akan pips. Mungode
.jpeg)
.jpeg)
0 Comments