Silallan yanar gizo-gizo (Crypto currency) sun samo asaline
tun shekarar dubu biyu da tara (2009), a dai-dai lokacin da wani mutum mai suna
satoshi nakamoto ya wallaba sulen farko wato Bitcoin (BTC), wanda kuma daga
bayane akai ta samun karuwar wadan sulallan har izuwa yau. Bitcoin shine farkon
sulen da aka fara kirkira, kana kuma daga bisani sauran sulallar yanar
gizo-gizo suka fara bayyana, kamar irin su etherium (ETH), litcoin (LTC) da makamantansu.
An kirkiri wadannan sulallan ne ba dan komai ba sai dan
saukaka kulla kasuwanci tsakanin kasa da gasa, domin kafin zuwan wadannan
sulallan dolene inza kai siyayya, ko kuma kana son ziyartar wata kasar
kamallaki irin kudadensu, ba dannan komai ba sai dan wannan kasar bazata yarda
da irin kudinka ba. Wannan dalilin yasa dayawa daga cikin ‘yankasuwa dake fadin
duniya nashan wahala wajen canza kudi atsakaninsu, saboda in kana son tura kudi
wata kasar, bazaka iya turashiba kaitsaye, dole sai kabi wasu ka’idoji kafin
kudin su isa inda z aka turasu.
Satoshi nakamoto wannan matsalar yakalla, sai yai tunanin mai
zai hana ace asamar da wani abu tsayayye guda wanda duk duniya zata yarda dashi
a matsayin kudi, tunda dai ance kudi shine duk wani abu da mutane suka yarda
dashi amatsayin abunda zasuringa yin siyayya da shi a tsakaninsu. Wannan shi
yabawa satoshi dama wajen ganin cewa ya kirkiri BTC, domin yazama kudi nafarko
da duniya zataringa amfani dashi wajen kula kasuwancinta da kuma al’amuranta na
yau da gobe wadanda suka danganci kudi.
Sai da BTC yadauki shekara guda dindi bai ko motsa daga
farashin da yake ba, domin a wannan lokacin doniya batasanma amfanin saba da
kuma irin saukin da yakawo mata ba. Farashin BTC yafara motsawane a shekara ta
dubu biyu da goma (2010), yayin da duniya tafara fahimtar dinbin alkhairin da
ke tattare dishi BTC din, domin duniya tafara fahimtar cewa lallai ba makawa BTC
dinnan ba karamin saukakawa harkar kasuwanci zai ba.
Kafin zuwan wannan kudin na BTC ya kasance idan mutun zai
tura da kudi wata kasar, to dole ne sai dai yasamu wani kamfanin da zasu canza
masa wadannan kudaden nasa izuwa kudin wannan kasar da zai tura, baya gannan
kuma idanma ya tura kudin yakan dauki wasu ‘yan kwanaki kafin kudin ya isa inda
ya tura su. Sannan in kudin ya isa inda yaturasun sai ansamu gibi a kudin,
saboda ladan aiki da wannan kamfanin zasu dauka da kuma makamantansu.
Lokacin da BTC ya bayyana, sai yazamana cewa baka da wani
bukatar canzashi izuwa kudin wata kasa yayin turashi, sannan kuma kaitsaye zaka
iya turawa mutum shi da kanka sabanin da da sai dai wani kamfanin ya turama
dashi, kuma abun burgewarma shine da katurawa mutum acikin ‘yan awanni kalilan
zai isa izuwa gareshi, sabanin da dasai ya dauki wasu kwanaki. Wannan saukin
duniya takalla da ke tattare da BTC, yakan yasa duniya batai wata-wata ba tai
saurin amanna da shi, domin magance damuwarta abangaren hada-hada da kudi.
Bayan BTC yasamu karbuwane aduniya sannan kuma wasu sababbin
kudaden yanar gizo-gizon sukai ta bayyana, amman saidai yar yanzu babu wanda
yakama kafar BTC domin wai hausawa nacewa nagaba yayi gaba na baya sai dai
labara.
Wannan shine dan takaitaccen tarihi game da sulallen yanar
gizo-gizo (crypto currency), muna fatan ‘yan uwa da abokan arziki sun amfana da
wannan dan gajeren bayanin namu. Idan har kunji dadinwannan bayanin namu to
kusanar da mu a contact page dinmu da ke kasa kadan da wannan sakon, domin kara
mana kwarin gwiwa. Mungode, a-mangourp.blogspot.con na kune har kullum.
0 Comments