Ka’idar yacce ake samun kudi a YouTube itace, dole sai mutane sun kalli
bidiyoyinka da kadora tsahon awa dubu hudu (4000) a abinda bai wuje shekara
gudaba, sannan kuma akalla kasamu subscribers guda dubu daya (1000) kafin YouTube
su fara biyanka, Wannan dalilin yasa dayawa daga cikin mamallakan YouTube
sarewa, saboda atunaninsu baza su taba samun kudi da YouTube ba, mutakar dai
basu cika wannan sharunba.
Yin kokarin cika wannan sharadin nasu abune me kyau, ammanfa musani cewa
bawai lallai sai YouTube sun fara biyanka bane zaka fara samun kudi da channel
din ka faba. Akwai miliyoyin hanyoyi da zaka iya fara amfani da su dan samun
kudi a YouTube tunma kafin su fara biyan naka, kadan daga cikinsu sune kamar
haka.
1.
Amfani da YouTube din wajen jawowa
kanka customers
Yin bidiyo hanyace mai kyau wajen yada kasuwancinka ga al’umma. Za ka iya
amfani da YouTube wajen gabatar da kanga da kuma irin kasuwancin da kake yi ga
al’umma, zaka kuma iya nunawa al’umma
irin abunda kasuwancinka ya kunsa, ta hanyar nuna musu irin kayanka da kuma
irin nagartar da suke da shi.
Acikin wannan bidiyon naka, zaka iya bada cikakken adireshinka da kuma
lambar yawarka, domin saukakawa mutane in suntashi bukatar kayanka. Hakan zai
kara taimakawa wajen kara yawan customers dinka da kuma watsa kasuwancinka a
cikin jama’a. kunga kenan da yiwuwar samun kudinka ya kara nin kuwa akan na
baya, tunda zaka samu Karin kostomas.
2.
Dillanci (Affiliate Marketing)
Dillancin (affiliate marketing) wani tsarine da mutum zai ringa tallatawa
wani mutumin ko wani kamfanin kayansa, ta yadda in wani mutumin yasai wannan
kayan a ta dalilinka, to wannan mutumin ko kamfanin da kayiwa talla, za su biya
ka ladan aikin da kai musu..
Manyan kamfanunnuwa irin su amazo, e-bey da dai sauransu na da wannan
irin tsarin. Zakayi rijista da su, sai subaka dama karinga tallata musu
kayansu, duk kuma wanda ya siya a ta dalilinka to za su biyaka ladan aiki.
Mutum zai iya amfani da wannan damar wajen samun kudi a YouTube. Yadda
mutum zai yi shine, kafara zabar bangaren da kake ganin cewa zaka iya tallatawa
wannan kamfanin. Misali, ace mutum ya kware akan kayan lantarki, to sai yai
rigista da amazo ko dai wani kamfani da suke da irin tsarin dillanci (affiliate
marketing) sai ya tsara bidiyoyinsa akan kayan lantrki, misali yazamana ceya
yana bayani akan yadda ake amfani da kayan lantarki, ya kuma yi bayani akan
mahimmancin amfani da su, ya kara kuma da bayani akan karkon wannan kayan. Sai
ya dora akan YouTube channel dinsa, wanda a cikin description na wannan bidiyou
din sai yasa link dinsa na dallancinsa (affiliate marketing) hakan zai taimaka
ga duk wanda yaji dadin bayaninsa in ya tashi shiya to zai amfani da wannan link din nasa yasiya, wanda hakan
shi zaisa wannan kamfanin suringa biyansa.
Kunga kenan da wannan hanyar mutum zai iya fara samun kudi a youtube
tunma kafin su fara biyansa, domin zai ringa samun kostoma ta channel dinsa
bama tare da ya fita wani waje yanayiwa muta ne bayaniba.
3. Talla
Ga Manyan Kamfanunnuwa
Magana ta
gaskiya mutum na bukatar tarin jama’a da yawa kafin manyan kamfanunnuwa suringa
bashi talla, amman hakan ba zai hanaka amfani da wannan damar ba wahen fara
samun kludi ba a YouTube ba, tun kafin su fara biyan ka ba, kai dai kawai kayi
kokari wajen ganin cewa kanayin aiki mai kyau a channel dinka domin hakane
zaisa mutune suyi ta zuwa channel dinka domin kallo, wanda kuma hakan ake
bukata agareka.
Domin fara
karbar talluka akwai wasu sharuda da yakamata ace mutum yacika: zaka gabatar da
kanka da kuma YouTube channel dinga ga wannan kamfanini, yazamana cewa abunda
kake dorawa a channel dinnaka yana da alaka da abinda wannan kamfanin yake
siyarwa. Kayi cikakken bayani akan irin jama’ar da kake ma’amala da su, musali
yawansu da kuma alakarsu da kasuwancin wannan kamfanin. Idan kana da wani
dandali a wata kafar sada zumunta zaka iya hada musu da ita domin kara tabbatar
musu da cewa kana da jamar da zaka iya tallata musu kayansu. Kanuna musu cewa
kafi damuwa akan bunkasar kamfaninsu bawai kudinsu kake so ba. Idan kataba
amfani da wani kayan nasu, to kasanar da su, ka kuma gaya musu ra’ayinka akan
wannan kayan nasu.
Wannan sune
kadan daka cikin kad’idojin da mutum yakamata ya kiyaye yayin neman talla a
wajen wani kamfanin a online. Da zarar kagama cika sharudan nasu, to kamfanin
za suba ka bana dinsu kana tallata musu, su kuma suna biyan ka ladan aikinka.
Kunga kenan da wannan hanyarma zaka iya samun kudi da talla a YouTube channel
dinka, tun kafin su fara biyanka.
Wadannan
kadan kenan daga cikin hanyoyin da mukai nazari akan su kenan da mutum zai iya
fara amfani dasu domin fara samun kudi a youtube din sa tunkaminma ace sunfara
biyansa.
Samun
Nasara Akan Kasuwancin YouTube
Kamar yadda
tsarin nasarar kowane irin kasuwanci ta kasance akan jajurcewar sa, haka shima
nasarar samun kudi a YouTube yake, domin ya ta’allaka ne akan irin jajurjewar
mutum da kuma kwazonsa wajen ganin ya tara jama’a a channel dinsa, ta hanyar
tsara musu abubuwa masu amfani, wadanda zasu kayatar da su, sukumu nishadantar
da su.
0 Comments