Shin da gaske kanason fara kasuwan cin
yanar gizo-gizo (online business) amman bakasan taya zaka fara ba, inko hakane
to ka zo inda ya dace, domin a wannan rubutun zamuyi bayani akan hanyoyi guda
biyar da mutum zai bi ya kai ga cin nasara yayin fara kasuwancin yanar
gizo-gizo (online business).
A wannan rayiwar tamu akwai hanyoyin
samun kudi a yanar gizo-gizo (online business) da yawan gaske, kadan daga cikin
su sune, online surveys, affiliate marketing, pay-per-click (PPC) advertising
dadai sauransu. Wannan kadan daka cikin hanyoyin da zasu iya canza rayiwar
mutum ne daga matsayin da yake izuwa matsayi na sama.
Saboda haka idandai har mutum nason samun
kudi masu yawan gaske kuma cikin sauki, tofa lokacin yazo, domin mutum zai iya
fara kasuwancin yanar gizo-gizo dakansa domin samawa kansa haryar kudin shiga.
Bari muga hanyoyi guda biyar masu
muhimmanci da mutum yakamata yabi yayin fara kasuwancin yanar gizo-gizo (online
business).
1. Ilimi
Hanyar samun nasara akowane irin
kasuwanci bama wai kasuwancin yanar gizo-gizo (online business) ba shine
illimi. A duk lokacin da yaza mana cewa mutum na son fara kasuwancin yanar
gizo-gizo (online business) matakin farko da yakamata ya dauka shine, neman
ilimi akan wannan kasuwancin, ta hanyar buncike da kuma tambayar masana
aharkar, badan komaiba sai dan hakan zai tai maka mishi wajen kaucewa kananan
matsaltsalun da ka iya jamai asara.
Samun cikakken ilimi akan kasuwancin da mutum
ke son farawa na iya taimaka masa wajen habbaka kasuwancinsa tahanyar bijiro da
sabbin tsare-tare a kasuwancin nasa.
Ka/ki sani wani lokacin neman temakon
‘yan uwa ko abokai dan gane da fara wani kasuwancin ka iya kawowa mutum nakaso
a kasuwancinsa, domin ta iya yiyuwa su abisa rashin fahimtar kasuwancin su gaya
mai wani mummunan abu game da gasuwancin, wanda zai iya saka shi jinkiri koma ya
fasawa. Amman in masana katabbaya to daman su sun dade suna harkar, su zasu iya
gayama ainahin abunda zai iya faruwa da wannan kasuwancin, domin su ganaune ba
jiyau ba a harkar.
Dadin da dawa shine, yayin fara
kasuwancin yanar gizo-gizo yana da kyau ace kazafi bangaren da ke da jama’a
sosai, domin hakan shine zai baka damar samun kudade masu yawan gaske.
2. Mallakar shafi (website or social media)
Domin fara kasuwancin yanar gizo-gizo
kana bukatar jama’a, wadanda za su yarda da kai. Wadannan mutanen sune zakayi
amfani da su yayin samarwa da kanka hanyar kudin shiga, domin yawancin hanyoyin
samun kudi a yanar gizo-gizo sun ta’allakune da talla, talla kuma bazai yiyuba
in ba jama’a. wannan shine dalilin da yasa zaka bukaci website ko kuma social
media, domin saukaka tallanka cikin sauki.
Idan yazamanto cewa a wannan shafin naka
kana da jama’a da yawa, to zaka iya fara irin su affiliate marketing dadi
sauransu, domin fara kwashe romon demokaradiyyarka.
3. Saka talla a shafin ka (website)
Bacin ka mallaki shafinka (website), ka
kuma yi kokarin tara jama’a acikinsa mataki nagaba shine fara saka talla
acikinsa domin afara biyanka. Watakila wani/wata ya/ta ce to taya zansamu tallan,
wannan abu mai sauki ne, domin goggle suna bawa duk wani wanda ya mallaki shafi
talla ta yadda duk mutum daya in yashiga wannan shafin naka yagani goggle zasu
biya ka, haka zalika kuma in yasiyi wannan abunda da kai talla, goggle zasu
kara ninkama kudinka.
Baya ganan kuma, manyan kamfanunnuwa irin
su amazon zasu iya baka talla ta yadda duk wanda ya sai kayansu a ta dalilinka
zasu biya ka. To ta wannan hanyar zakaringa samun kudin shiga.
4. Lura da wadanda suke irin kasuwancinka
Yana da kyau ace karinga lura da wadanda
suke irin kasuwancinka domin idan yazamana cewa sunfika bayani mai kyau game da
wannan kasuwancin naku to tabbas bamakawa hattana jama’arkama gunsu zasu koma,
domin su mutane sunaso ka gamsar da su kafin su siyi abinda kake tallatawa.
5. Hakuri
Abu nakarshe shine, dole mutum yai hakuri
kafin ya kai ga nasara. Babu yacce za ai mutum yace daga fara kasuwancinsa a
yau ba, kuma wai yai tunanin yau din ko gobe zai fara samun kudi ba. Dole sai
kayi hakuri ka kuma tsaya tsayin daka ka gina kasuwancinka kafin kafara cin
moriyarsa.
Wadannan sune kadan daga cikin hanyoyin
da in mutum ya bisu ya kuma kiyayesu, to insha Allah zai kai ga cin nasara
0 Comments