A wannan zamanin, mutum zai iya fara neman kudi da wayar
hannunsa, ko kuma computer dinsa batare da ya wahalar da kansa ba, domin akwai
hanyoyin samun kudi da yawa cikin sauki a wannan zamanin, sabanin zamanin baya.
Wani abun burgewa da wannan zamanin shine zaka iya fara
kasuwancinka na yanar gizo-gizo (online business) daga duk inda kake a fadin
duniya, ba tare da kana da wani jari ba, abunda kake bukata kawai shine tsari
mai kyau domin dorewar kasuwancinka.
A wannan zamanin akan samu mutane dayawa da suke gudanar da
kasuwancinsu a yanar gizo-gizo (online business) batare da sun taba sa ko sisin
su ba, domin a yanzu akwai hanyoyin samun kudi da yawa a yanar gizo-gizo da
basa bukatar ko sisin ka. Misali, za ka iya fara blogging wato rubuce- rubuce a
kyauta ta hanyar amfani da wordpress, daga bisani kuma karinga karbar talla
daga google suna biyanka. Ko kuma karinga yiwa manyan kamfanunnuwa na duniya
talla suna biyanka, kamar su amazon da dai sauransu.
Bari muga hanyoyi guda hudu da mutum zai iya bi domin fara
kasuwancin yanar gizo-gizo (online business) batare da yasa ko kwandalarsa ba.
1. Dillanci (Affiliate marketing)
Dillanci (Affiliate marketing) shine kusan hanya mafi sauki
da mutum zai ringa samun kudi da shi a yanar gizo-gizo. Baka da bukatar
mallakar kayan siyarwa bare mahallin da za ka ringa ajjesu. Abunda kake bukata
kawai shine, kazabi kamfanin da kaga yayi maka, sai kai rijista dasu domin fara
tallata musu hajarsu, duk wanda ya siyi hajarsu a ta dalilinka, to zasu baka
tukwici.
Domin saukakawa kanka wajen samun jama’ar da zaka ringa
tallata hajojinka, kana bukatar bude shafi a yanar gizo-gizo (website), dandali
a kafafen sada zuminta (social media platforms) dadai sauransu. Za kayi amfani
da sune domin tara jamar da zakaringa yiwa talla akan abunda kake dillanci.
Atakaice dillanci shine tallatawa wani ko kamfani kayansu,
idan mutum ya sayi wannan kayan nasu a ta dalilinka, to wannan kamfanin ko
wanda kayiwa tallan zasu biyaka la’ada.
Babban kalubale a wannan aikin shine, kokarin tara jama’ar da
za karinga yiwa talla. Yacce zaka sa mesu cikin sauki shine, karinga kokarin
tsara Magana mai dadi, wacce zataringa burge muta ne yayin saurararka. Ya zamto
cewa kana iya gamsar da jama’ar ka akan abinda kake so suringa siya. Hakan zai
taimaka maka wajen jawo jama’a izuwa shafink, da makamantansu dan ganin abinda
kake tallatawa.
2.
Rubuce-Rubuce (Blogging)
Idan kana da
ra’ayi ko sha’awa akan wani abu, to zaka iya fara rubuce-rubuce akan wannan
abun domin saukakawa kanka wajen gabatar da bayani.
Nasan ta iya
yiwuwa mutum yai mamakin cewa taya za’ai mutum yaringa samun kudi da
rubuce-rubuce. Wannan ba abun mamaki bane domin kuwa zamuga cewa akwai gidan jaridu
dayawa da suke samun kudi ta hanyar rubuce-rubuce.
Bari muga
kadan daga cikin hanyoyin da mutum zai iya bi domin samun kudi da rubuce
rubucen da zai ringa yi.
i. Talla ga google (Google Adsence)
Babu wata
hanya da tafi bawa kamfanin google kudi a kas kamar hanyar tallace-tallace. Manyan
kamfanunnuwa na duniya na biyan kamfanin google magudan kudi domin su tallata
musu manhajarsu, ba dan komai ba sai dan yawan jama’ar da kamfanin google suke
da shi.
Google na da
wani tsari da ake kiransa da google ads. Idan mutum ya kasance cewa yana da
wani shafi (website) ko wani dandali a yanar gizo-gizo (online forum) da yake
rubuce-rubucen sa (blogging), zai iya nemar kamfanin google suringa bashi irin
wadannan tallukan da suke karba daga manya manyan kamfanunnuwa domin shima ya
tayasu tallata wadannan tallukan. A duk lokacin da wani ko wata yashiga wannan
shafin naka yaga wannan tallan, to google zasu biyaka. Haka zalika duk wanda ya
danna wannan hoton tallan dan ganin Karin bayani, to google zasu nikkama
kudinka, kuma koda acema a kuskure ya danna wannan hoton tallan.
ii. Dillanci (affiliate marketing)
kamar yadda
ya gabata a baya cewa, zaka iya yiwa manyan kamfanunnuwa talla kamar irin su
amazon da dai sauransu, duk lokacin da wani ya sai kayansu a ta dalilin ka,
wannan kamfanin za su biya ka la’ada. Za ka iya amfani da hanyar rubuce-rubucen
ka wajen tallatawa jama’ar da ke bibiyar ka irin kayan da kake dillanci.
3.Sa bidiyo a youtube
Zaka iya yin
amfani da bidiyo wajen ya da kasuwancin ka a fadin duniya. Za ka kuma iya yin
amfani da wannan hanyar ta yin bidiyo domin jawo mutane izuwa shafinka, ko
dandalinka, domin ganin irin abunda kake tallatawa, wanda ta hakan zaka iya
samun Karin masu siyan kayan da kake dillancin, ko kuma masu ganin tallan da
google suke sama a shafinka.
4. koyarwa
Idan har akwai
wani abu da ka iya, kuma kake ganin cewa ka kware a kan wannan abun sosai, to z
aka iya bude aji a yanar gizo-gizo (online) domin koyar da wannan abun. Zaka iya
raba darusan na ka gida-gida, in yaso zaka iya sa darasin farko in mutum ya
gamsu da darasin farkon naka sai ya biyaka dan ka tura masa ragowar.
Wannan hanyar
ni da kaina na gwadata, kuma alhamdullillah domin na samu alheri da ita. Kai dai
kawai kai kokari kaga cewa kana gabatar da bayanai masu mahimmanci.
Wadannan sune
kadan daga cikin hanyoyin da mutane zasu iya bi domin fara neman kudi a yanar
gizo-gizo ba tare da mutum ya sa ko sisin sa ba. Allah yasa mudace.
0 Comments