TARIHIN FOREX
Kasuwar forex ta samo asaline tun lokacin da wasu tsirarin mutane ke taimakawa al'umma wajen kulla cinikaiya atsakanin su, tahanyar samo musu wanda za su siya ko siyar da kayansu a wajen su. A yau Wadannan mutanen sune ake kiransu da Brokers (kamar dillalai kenan).
Kafin samuwar kudi a shekarun baya, ban gishiri inbaka manta shine hanya mafi shahara da mutane ke bi domin kulla kasuwanci. Mutum kan canzar da hatsinsa domin samun dawa ko kuma samun duk abunda yake bukata.
A lokuta mabambanta mutane kansha wuya kafin su iya canzar da abunda ke hannun su dan samun abun bukatar su, domin kuwa yakan iya zamtowa cewa, shi wanda kake son canzar abun hannunsa baya da bukatar naka abun, ko kuma shima wani abun da ban yake da bukata ba wannan abin hannun na kaba. Alal misali ace, kana da shinkafar da kake son bawa wani domin ya baka wake, amman shi mai waken baya bukatar shinkafa, alkama yake buqata ko wani abun da ba shinkafa ba, domin ta iya yiwuwa shima yana da shinkafar.
Wannan dama wasu dalilan ne ya sanya mutane shan wahala kafin su iya samun abunda suke bukatar, hakan yasa musu tunanin yaka mata ace su tsayar da wani abu tsayayye wanda kowa ya yadda dashi domin a ringa kulla cinikayya da shi, sabanin da dasu ke amfani da ban gishiri inbaka manda.
Gold, Azurfa da kuma tagulla, sune abubuwan da mutane sukafi aminta dasu yayin kulla kasuwanci a tsakanin su, wanda hakan ne yasa sama da shekaru Dubu biyu (2000) da suka gabata Girkawa da mutanen kasar misrah suke canji in canza da wadannan abubuwan a dai-dai lokacin da suka fahimci cewa darajar su zata iya tashi. Su kanyi kokari suga sun mallaki daya daga cikin wadancan abubuwan, a lokacin da ya zamana cewa sunyi karancin a hannun al'umma ta yacce idan na hannun al'ummar yakara zai zamana cewa su kadai ne ke da nau'in wannan abun ( wato gold, azurfa ko tagullar kenan), lokacin da ya zamana cewa al'umma na buqatar sa sai su kara masa taraja akan yadda suka mallake shi a baya domin cin riba.
Tahaka ne sauran kasashe dake sassan duniya daban-daban suka fara fahimta wannan tsarin, hartakai suma sunfara wannan canji in canza din.
Kasuwar forex da aka fara budewa ta farko itace wacce aka bude a Amsterdam shekaru 500 da suka gabata kenan, wanda hakan yabawa mutane da ke sassan duniya daban-daban damar canza kudaden su a lokacin da suka fahimci cewa darajar kudin wata kasar zai tashi ko sauka.
A 1913, kasuwancin forex yakara samun bunkasa daga kaso 3 zuwa kaso 71 a cikin shekaru goma a kasar London. Kaso 50 na kasuwancin forex anfi yinsane akan pound Sterling. A shekarar 2013 pound Sterling ya zamto kudi na hudu da akafi siya da siyarwa a kasuwar forex bacin Dalar Amurka, Euro da kuma Japanese Yen.
Bayani acikin video
Wannan kadan kenan daga cikin tarihin kasuwancin forex kenan, wanda kuma shine mafarin karatun mu. Bayan sanin wannan dan takaitaccen tarihin kuma, yana da kyau musan me ake nufi da kasuwancin forex, sannan kuma ya ake gudanar da shi.
Menene forex, ya kuma ake kasuwancin sa
Kasuwar forex tamkar kasuwar wafa ce (kasuwar canjin kudi), bambamcin su kawai shine, ita kasuwar wafa kasuwace ta zahiri, ita kuma kasuwar forex a yanar gizo-gizo take.
Kasuwar forex kasuwace da za ta bawa mutum dama ya canza kudin sa izuwa kudin wata kasar batare da yaje ko ina ba. Mutane kan ribaci wannan kasuwar tahanyar siyan kudin wata kasar a dai-dai lokacin da suka fahimci cewa darajar wannan kudin zata iya dagawa, su kuma siyar da shi a dai-dai lokacin da suka fahimci cewa darajar wannan kudin zai fadi.
Abun tambayar anan shine, ta yaya mutum zai iya gane lokacin hawa da kuma saukar farashin kudin ko wace kasa? Wannan shine abunda za mu koyar da ku kenan a wannan shafin namu na a-mangroup.blogspot.com, saboda haka sai ku kasance a tare da mu domin ganin yadda ake ganowar.
Mungode, sai mun hadu a rubutun mu nagaba, inda zamu kawo muku bayani akan currencies
.jpeg)
0 Comments