Ya tabbata cewa akwai hanyoyin samun kudi da yawa wanda kasuwancin silallan yanar gizo-gizo (Crypto currency) yazo dasu, amman wadanda suka fi shahara agaremu sune siye da siyarwa. Mukan sayi coin ne yayin da farashinsa ya sauka, sannan kuma mu sai dashi a lokacin da farashin sa ya tashi.
Sai dai dayawa daga cikin 'yan uwa da kuma abokan arziki basu san taya za su iya gane lokacin da coin zai sauka ba, ballanta na su siya. Haka kuma zalika basu san lokacin da zai tashi ba, ballantana in ya tashin su siyar domin cin riba.
Wannan dalilin yasa a-mangroup suka shirya tsab domin gabatarwa da 'yan uwa da kuma abokan arziki wasu 'yan takaitaccun lakcoci game da wannan matsalar, wala'alla a samu wasu kadan daga cikin 'yan uwa su amfana ko fa'idantu da hakan.
Amman kafinnan, yana da matukar mahimmanci ace mutum ya karanta wadannan rubutun namu guda biyu, domin kara samun guziri, wato; wai meyasa banyi kudi ba a Crypto har yanxu da kuma hanyoyin da mutum ya kamata yabi yayi fara kasuwancin
Mundin dai ya zamana cewa ka/ki nason samun kudi ta hanyar siye da siyarwa a kasuwancin silallan yanar gizo-gizo (Crypto currency), to wajibine ka/ki san yanayin hawa da saukar kowane coin a kasuwa, domin ta hakan ne kadai mutum zai iya cin riba a wannan kasuwancin.
Abun tambayar anan shine, taya mutum zai iya gano lokacin da coin zai sauka ko kuma tashi, domin sanin matakin da zai dauka yayin da yake kasuwa.
Magana ta gaskiya itace, babu wani mutum da ya isa ya gano hakikanin inda farashin kasuwa zai yi, domin a wasu lokutan kasuwa ta kan yaudari mutane agame da abunda suke zaton farashin ta zai kasance. Duk abinda mutum zaiyi domin gano inda farashin kasuwa zaiyi, zatone kawai. Amman amafiya yawan lokuta, wannan zaton na iya zama gasiya, wanda zamu iya cewa a cikin kaso dari na duk zaton da akewa kasuwa yayin yin analysis, kaso saba'in 70% na tabbata dai-dai. saboda haka idan mutum yayi analysis dinsa kuma yaga akasan abunda yagano cewa farin kasuwa zai zama bacin shigarsa kasuwa, kar ya wani damu domin da man munce zato ne akewa kasuwar, dan dama babu Wanda yasan gaibu bacce Allah kadai.
Akwai wasu hanyoyi da yawa da ake bi domin iya gano halin da coin zai shiga anan gaba, wato shin zai tashine? Ko kuwa sauka zaiyi? Daya daga cikin wannan hanyoyin itace ake kiranta da fundamental analysis.
Fundamental analysis wata hanyace da mutane suke iya bi domin bincikar ingancin coin da kuma kyawunsa. Dole sai coin ya tabbata cikakken coin kafin ma mutum ya fara tunanin sa Kudin sa akan wannan coin din, saboda gudun fa dawa hannun 'yan damfara.
Saboda haka wajibine ga duk Wanda yake son fara kasuwancin silallan yanar gizo-gizo (Crypto currency) yazamana cewa yana da ilimin da zai iya tantance hakikanin gaskiyar ko wane irin coin. Shin wai ma kuwa coin dinnan akwaishi kuwa ko kuwa yaudarace? In akwaishin shin mai kyau ne ko jabi ne? Shin yana da gobe me kyau ko kuwa jirgin dankaro ne? Wadannan sune abinda mutum ya kamata ace ya fara sani kafin ma gano cewa shin yaushe wannan coin zai tashi ko sauka.
Fundamental analysis ne hanyar da mutum zai iya bi domin samun amsoshin dukka wadancan tambayoyin nasa. Mafiya yawan lokuta mukanyi fundamental analysis ne yayin da muke shirin siyan wani coin, dan mu rikeshi na lokaci mai tsaho domin samun gwagwgwabar riba akan sa. Saboda haka, ga duk wanda yake da burin kawai ya sai coin ne ya kuma ajje shi na lokacin mai tsaho (investing) domin cin riba a gaba, to fundamental analysis ne yaka mata ace yafi mai da hankali akansa, domin gano goben wannan coin din, dan kar yaje ya sai yayin banza (shit coin) yai ta dakon abinda ba zai haifar masa da da me ido ba.
Yayin gudanar da fundamental analysis akwai wasu jiga jigan abubuwa da mutum ke da bukatar dubawa yayin samun gamsashshun amsoshin tambayoyin sa. Kadan daga ciki sune kamar haka;
1. Tabbatuwar coin din da mutum zai siyan
Wajibine ga mutum ya fara tabbatarwa akan cewa wannan coin din da yake/take son siya, ya tabbata akwaishin ko kuwa yaudarace, domin akan samu 'yan damfara sukawo coin din da babu shima kwata-kwata wanda in mutum ya siya bazai taba iya siyar da shi ba. Yanzu abunda 'yan yaudarar sukeyi shine, sukan samu wani coin din da suka ga mutane sunfi siyansa, sai sukirkiri jabin wannan coin din, wanda in mutum bai ankara ba sai yaje ya sai wannan jabin.
Misali guda daya da zamu bayar game da wannan gabar shine, akwai wani coin mai suna daex wanda ga duk wanda yasan coin, yasan cewa coin din yana da gobe me kyau, to amman matsalar da aka samu shine, ansamu wasu maha'intan sun kirkiro jabin coin din wanda suka sa masa suna daex trade, wanda hakan yasa dayawa daga cikin mutane sunje sun siyi wannan daex trade din a memakon daex na asali din.
To haka 'yan danfarar nan sukeyi. In suka tashi, suna dan kadan zasu kara a gaban sunan coin din na asali kawai sai suringa yaudarar mutane da shi. Dan haka wajibine ga duk wanda yake son siyan wani coin, ya fara tabbatatwa cewa wannan coin din akwai shi tukunna, sannan kuma in akwaishin yatabbatar da cewa na gaske ya siya ba wai jabin ba.
Taya mutum zai gane cewa coin din d zai siya akwaishi da gaske, kuma na gaskiya ne ba wai jabin bane?
Domin samun gamsashshiyar amsa game da wannan tambayar, wajibine ga mutum ya samawa da kansa amsoshin wadannan tambayoyin masu zuwa.
Shin wannan coin din akwaishi kuwa a kasuwar Crypto? In akwai shi, to a wace kasuwa yake? shin coin din yana da liquidity a wannan kasuwar kuwa? In yana dashi, shin zan iya siyansa ko na sai dashi a wannan kasuwar batare da wata matasala ba? Su wane suka kirkiri wannan coin din? Su wane suka fiya siyan wannan coin din? Menene utility na wannan coin din? Dan me aka kirkiri wannan coin din?
Muddin dai mutum ya samu gamsasshun amsoshi game da wadannan tambayoyin to zai iya tabbatar da cewa wannan coin din dagaskene akwaishi ko kuma babu shi. Idan har yaza mana cewa wannan coin din akwaishi a wata kasuwar Crypto din, kuma ya za mana cewa za ka iya siyansa ka kuma sai dashi a wannan kasuwar batare d wata matsala ba, to lallai babu shakka wannan coin ya tabbata cewa akwaishi. Sabanin hakan kuma mutum ya san cewa akwai yaudara akan wannan coin din.
Abun tambayar anan shine, taya mutum zai samu dukkan amsoshin tambayar sa game da coin din da yake son siya? Ko wane coin yana da abinda muke kira white paper a turance. Za kasamu duk wani bayani game da wannan coin din. Abunda mutum kawai zaiyi shine yashiga Google.com sai yai rubuta white paper na wannan coin din. Misala BTC white paper. In mutum ya samo wannan white paper din sai ya zauna ya karantata a tsanake.
Baya ganan kuma, mutum zai iya bibiyar wadanda suka kirkiro wannan coin din a kafafen sada zumunta (misali:- Telegram, Twitter, YouTube dadai sauransu) domin samun karin bayani game da samun amsoshin tambayar sa.
2. Shin coin din yana da Gobe mai kyau kuwa?
Bayan mutum ya gama tabbatarwa akan cewa wannan coin din ya tabbata cewa akwaishi, sai kuma yai kokarin gano cewa shin wannan coin din yana da gobe me kyau kuwa ko kuwa a'a? Taya kenan
Domin sanin ya goben coin din da mutum zai siya, yazata kasance, akwai wasu abubuwa da muke dubawa kamar haka:-
i. Yawan adadin wannan coin din a kasuwa (Total supply)
Idan har yazamana cewa wannan coin din da mutum zai siya adadinsa bai wuce hankali ba, to tabbas akwai yiwuwar in har mutane suka karbeshi hannu bibiyu, wannan coin din zai bada kudi akas. Amman muddin yazamana cewa adadin wannan coin din ya wuce hankali, to tabbas ko da ace mutane sun karbe shi hannu bibbiyu, farashin zai wahalar tashi. Saboda a tsari na dokar kasuwanci shine " Duk lokacin da adadin kaya yai kasa, kuma akwai mabukata to dole farashin wannan abun ya tashi. Sabanin hakan kuma, farashin nasa karyewa zai yi"
Dan karamin misali shine, kafin Baba buhari ya hau mulki Nigeria, shinkafa 'yar hausa bata da wani tsada, Amman bacin ya rube bodar iyaka da yahau kan karagar mulki sai shinkafa'yar hausa ta nunnunka Kudin ta, mai yasa saboda yawan masu siyan ta ya karu.
Baya ganan kuma, a duk lokacin da adadin coin ya wuce hankalin mutane, kulura da kyau mutane basa son siyan wannan coin din, saboda sunyi imani dacewa ko dama ace ana siyan sa, to zai dade farashin sa bai tashi ba. Muddin kuma mutane sunajin tsoron siyan coin wannan alamace da ke nuna cewa coin din bashi da mabiya da yawa, in kuwa ya za mana cewa wannan coin din bashi da mabiya daya zai dade kuwa bai tashi ba, domin kuwa babu masu siyansa akai-akai. Misalin irin wannan coin din shine CMDX.
ii. Liquidity
Liquidity shine kudin da za asawa wannan coin din, ta yadda in mutum yazo sai da wannan coin din, za'a dauka aciki a biyashi. Yana da kyau mutum ya duba adadin liquidity na wannan coin din da zai siya. Idan har yazamana cewa liquidity na wannan coin din bashi da yawa, to kenan akwai yiwuwar karewar sa da wuri, in kuwa liquidity din coin ya kare, to fa baza kataba iya sai da wannan coin din naka ba, ya zama yayin banza. Domin ganin misalin hakan dannan wannan rubutun.
iii. Volume
Volume na nufin yawan siye da siyar war wannan coin din a kowace rana. Idan yaza mana cewa a ko wace rana ana iya siyan wannan coin sosai a kuma sai dashi, wannan shi yake tabbatar wa da mutum cewa wannan coin din yana da gobe me kyau. Domin kuwa tashin ko wane coin yana ala kantuwa da yawan siye da siyar warsa da akeyi a kullum.
In kuwa ya zamto cewa wannan coin din ba wani cika siye da siyar warsa ba a kullum, ko kuma inma ana siyan nasa a kullum din, to na kudi dan kadanne, to wannan na baka labarin cewa wannan coin din mutane basu yar da dashi bane shiyasa basa siyan sa. In kuwa har mutane basu yarda da coin ba, to kuwa babu makawa zai dade bai tashi ba.
Amman abun tambayar shine, tayaya zangano volume din coin din da nake son siya? Hanya guda daya mafi sauki itace mutum yashiga coinmarketcap, zai samu amsar tambayar sa.
iv. Partnership
Partnership na nufin irin manyan mutane ko manyan kamfanunnuwa da sukai tarayya da wannan coin din da mutum keson siya. Idan har yazamana cewa akwai wani babban kamfani ko wani babban mutum sananne a duniya da yake goyawa wannan coin baya, ko kuma kambanin yace ya yarda da wannan coin din a matsayin kudi, har ma ya amince da cewa zai ringa karbar wannan coin din a madadin kudi, to kuwa babu shakka wannan coin din zai tashi anan gaba, ba dan komai ba sai dan mabiya wannan kamfanin ko shahararren wannan mutumin zasuyi kokarin mallakar wannan coin din saboda mutumin ko kamfani.
v. Dalilin kirkiri wannan coin din
Muddin dai yazamana cewa wannan coin din yana da dalili mai kyau, to mutane zasuyi kokarin siyan wannan coin din, wanda kuma hakan zai iya daga darajar wannan coin din. Amman muddin yazamana cewa wannan coin din bashi da wani dalili mai kyau na kirkirar sa, to kuwa mutane baza suringa siyan saba, wanda hakan zai iya zama illa ga wannan coin din.
vi. Utility Value
Utility value shine dalilin da zai sa wannan coin din yaci gaba da tashi. Hakan kuma bazai yiwuba har sai mutane sunci gaba da siyan wannan coin din. Sai kaduba kagani shin wanda suka kirkiri wannan coin din sun masa tsarin da zai sa kullum mutane suringa siyan wannan coin din kuwa ko a'a. Misali, in mukai duba ga ETH ko BNB ko dace mutane basu siyesu ba dan cin ribi ba, dole ne wasu su siyesu dan cigaban kasuwancin su. Saboda a mafiya yawan kasuwannin da muke ma'a mala da su a Crypto zamuga gas fee din su ETH ne ko BNB, wannan dalilin yasa a kulum kwanan duniya ake siyan ETH ko BNB, wanda hakan shiyasa farashin su yake ta kara tashi lokaci bayan lokacin. Wannan shi muke kira da utility value.
Sai kaduba kagani shin coin din da zaka/zaki siya yana da wani tsarine da zaisa ace mutane suringa siyan sa akai-akai koda kuwa ace baza ai trading din sa ba.
Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da mutane yakamata ce sun dubane gabanin mallakar coin domin tabbatar da gobensa mai kyau.
3. Karyewar farashin coin.
Bacin samun tabbacin cewa wannan coin din da mutum ya siya yana da gobe me kyau, yana da matukar tasiri kuma yaringa bibiyar wannan coin din nasa da ya siya dan ganin cewa in wata matsala ta afku da ake sa ran cewa wannan coin din farashisa zai karye, yai kokarin sai dashi domin cin ribar abinda ya samu dan gudun asara kar ta shigo. Taya kenan?
i. Mummunan labari
A duk lokacin da mutum yaji ana fadar mummunan labari akan coin din da yasiya, to kamata yai yaikokarin buncikawa dan tabbatarwa, in har ya tabbata abinda ake fadi din gaskiya ne, to shawara mai kyau shine yai kokarin rabuwa da wannan coin din. Idan Kuma dama bai siya ba sai ya dan jinkirta, domin a wannan lokacin mutane zasuyi ta kokarin dawo da wannan coin din kasuwa saboda mummunan labarin da sukaji, wanda hakan kuma ba karamin karya darajar wannan coin din zai ba.
ii. Cire coin daga wata kasuwar
Idan har yazamana cewa wannan coin din da mutum ya siya ko zai siya, ancire shi daga wata kasuwar da yake ciki abaya, to akwai alamar wata matsala na faruwa, in mutum yariga da ya sayi wannan coin din to mafi kyautuwa ya sai da wannan coin din yajira yaga abinda hali zaiyi. In kuwa daman bai siya ba, to mafi kyau shine mutum ya dan jiraya yaga abinda zai faru da wannan coin din kafin ya siya din.
iii. Lokaci guda farain coin yai wawan tashi
A duk lokacin da mutum yaga cewa farashin yayi mugun tashi a lokaci guda, to kai kokarin rabuwa da naka, domin tabbas zai muguwar faduwa, inyaso da ya qara mugun faduwa sai ka kara siyansa. In kuwa dama can baka siya ba, to kar wannan mugun tashi dayake ya rudeka kace zaka siya, domin kuwa muddin ka siya a wannan yana yin, akwai yiwuwar asara ta shigo ciki.
iv. Yawan presale
Yawan presale na coin na iyasa mutane su mallaki wannan coin din da yawa, ta yadda ana sashi a kasuwa zasuringa dawo da shi, wanda hakan zai iya haifarwa d coin muguwar matsala anan gaba.
Wadannan hanyoyin sune kadan daga cikin hanyoyin da mutum zai iya bi yayin bincike fundamentally akan coin ga bannin mutum ya mallaki wannan coin din. Muna fatan wadannan 'yan bayanan namu su amfanar da wasu daga cikin 'yan uwa da abokan arziki.
Insha Allah rubutun mu nagaba zai kasance ne akan Technical analysis, ta yadda mutum zai iya gano hawa da saukar farashin coin yayin yin trading a Crypto. Mungode, a-mangroup na kune.
0 Comments