<\head>



Silallan yanar gizo-gizo (Crypto currency) wasu sabbin kudade ne da aka kirkire su a kan yanar gizo-gizo domin saukakawa 'yan uwa da abokan arziki wajen kulla kasuwanci a sassan duniya daban-daban. A shekarun baya kafin zuwan wadannan sulallan, idan za kai siyayya a kasar da ba taku ba, wajibine kacanza kudin da zakai siyayyar izuwa kudin wannan kasar, wanda kuma hakan ya kan dan wahalar da wasu 'yan kasuwar dayawa. 

Zuwan wadannan sulallan ya samar da sauki matuqa, domin kuwa ko wace kasa na iya amsar iran wadannan sulallan don kulla kasuwancin, mutukar dai wadannan sulallan sun cika ka'idar su na tabbata a matsayin sulallan.

Yatabbata cewa kudi shine duk wani abu da al'umma baki daya ta yarda dashi wajen siye da siyarwar su shine kudi. Wannan dalilin yasa kudi ke iya canzawa daga lokaci zuwa lokaci, ya danganta da irin zamanin da al'umma suka tsinci Kansu aciki.

A shekarun baya kafin zuwan kudi, anan kasar Hausa mun kasance muna kulla kasuwancin mu ta hanyar bangishiri in baka manta. Daga baya dalili yasa muka koma amfani da silallan irin su sisi, kobo, kwandala dadai sauransu. Bayan wani dan lokaci kuma wani dalilin yasa muka koma amfani da kudin takarda, daga bisani kuma wani dalilin yakara sa cewa muka koma amfani da kudin leda, kamar su naira biyar, goma da makamantansu.

A yanxu haka muna wani zamanine da ba ma da kudin za hiri muke amfani ba kawai, takai har da na badini muke amfani wato lambobi (Bank transfer). Yanzu akan iya fara kasuwancin har ayi agama baza kaga kudin zahiri ba ko daya, sai dai ai ta turawa mutane lambobin nan, to suma kudaden yanar gizo-gizo (Crypto currency) tamkar haka suke. Sai dai su sun banbanta da irin wadancan  lambobin na banki, domin su silallan yanar gizo-gizo suna da adadi, sabanin lambobin da banki ke amfani da su, hakan yasa silallan yanar gizo-gizo akowane lokaci darajarsu ke tashi amman su kuma lambobin banki nasu baya wani daraja.

Akwai da mammakin samun kudi dayawa ta hanyar amfani da manhajar silallan yanar gizo-gizo wanda tazo dashi. Kadan kaga cikin su shune kamar haka:-

i. Kirkiran naka silallan yanar gizo-gizon.



Babu shakka da ace mutum zai iya kirkirar nasa silallan yanar gizo-gizon, to kuwa d babu makawa yasamu hanya daya da zataringa bashi kudi akar, domin duk wanda zai sai wannan silallan yanar gizo-gizon naka kana da wani tukwici da zakaringa samu.

ii. Kirkiran kasuwannnan da ake hada-hadar silallan yanar gizo-gizon (exchanger).



Kirkiran kasuwar da za'a ringa hada-hadar silallan yanar gizo-gizo shine hanya mafi sauki ta samun kudi a wannan kasuwancin, domin duk wani coin da za a siya a kasuwarka sai anbiyaka wani dan kudi kadan da muke kiransa charges fee a turance kenan.

iii. Mallakar silallan yanar gizo-gizon akuma rikesu lokaci mai tsaho.

Abu mawuyacine ace mutum ya iya kirkiran nasa silallan yanar gizo-gizon, ko kuma kirkirar wata kasuwa dan kulla kasuwancin silallan yanar gizo-gizon. Hanya mafi sauki itace mutum yai kokarin ganin cewa ya mallaki wadannan silallan yanar gizo-gizon masu kyau, kuma sahihai domin rikesu na wani lokaci maitsaho. Babu yacce za ai mutum ya mallaki silallan yanar gizo-gizo masu kyau da inganci, ya kuma rikesu tsahon shekara biyu ko uku, kuma ace wai bai samu ribar ko da ace $1 daya ba. Hakan bazai taba yiyuwa ba.

iv. Yawan siye da siyar wa na silallan yanar gizo-gizon (Trading)



Siye da siyarwa na silallan yanar gizo-gizo zai bawa mutum daman yaringa samun kudaden shiga akai-aikai. Domin mutum zai siya ne a lokacin da darajarsu take kasa sannan kuma ya siyar lokacin ta ta tashi sama.

 Abun tambayar anan shine tayaya mutum zai iya gane sahihin coin domin siyansa ya kuma rikeshi na tsahon lokaci domin samun riba? Tayaya mutum zai iya gano hawa da saukar silallan yanar gizo-gizon domin fara siye da siyarwa dan samun Kudin shiga lokaci bayan lokaci? Kukasance damu a wannan shafin namu na a-mangroup.blogspot.com domin samun gamsashshiyar amsa.

Wadannan sune kadan daga cikin hanyoyin da mutum zai iya bi domin samarwa da kansa hanyar kudin shiga ta musamman a kasuwancin silallan yanar gizo-gizo. Munsani cewa hanya ta farko da ta biyu dayawa daga cikin mutane bazasu iya amfani da ita ba, amman ta ukun da ta hudun itace wacce mutane da yawa sukafi sani, suke kuma amfani da ita. Sai dai mafi yawan mutane kuma basu fiya yin amfani da ita ba akan yacce ta dace ba, hakan yasa dayawa daga cikin mutanen suke wahala matuka kafin susamu ko da $1 a matsayin riba ba.

Wannan dalilin yasa insha Allah zamu gabatar muku da sabon rubutunmu akaro naga ba dan yin bayani akan yacce mutum zai iya amfani da wadannan hanyoyin guda biyun domin fara samun nasa kudaden shigar a kasuwancin silallan yanar gizo-gizon (Crypto currency). 

Fatan zaku kasance da mu har izuwa lokacin da zamu wallafa muku wadannan mahimman bayanan. Mungode, a.mangroup.blogspot.com na kune...