Ta iya yiwuwa mutane da yawa sun yiwa kansu irin wannan
tambayar ta wai me yasa haryanzu banyi kudi a crypto ba, Sai dai kuma da yawa
ba lallaine su samawa da kansu gamsashshiyar amsa ba, domin da yawa daga
cikinsu balallaine su zarki kawunan su ba. Ta iya yiwuma suyi tunanin cewama
harkar crypto din shirme ce ko yaudara ce, wanda kuma a hakikanin gaskiya
zancen ba haka yake ba.
Dan uwa/’yar uwa masu albarka kusani cewa, muddin dai yazamto
cewa kun kwashe sama da shekara kuna saka kudadenku a harkar crypto kuma
yazamana cewa har yanxu baku samu wata riba ba, to gaskiya kusani matsalar ba
daga kasuwancin take ba, daga gareku take. Matukardai zaku cika sharudan fara
neman kudi a yanar gizo-gizo (online business) to kuwa bai kyautuba ace ku
kwashe sama da shekara guda ba kuna abu guda amman ace baku samu ko sisi ba. Shin
kuna son sani wadannan sharudan da zaka bi domin fara kasuwancin yanar
gizo-gizo (online business) maza danna wannan rubutun domin samun wannan ilimin
a kyauta.
Dayawa daga cikin mutane suna kuskurewa harkar crypto tun
daga lokacin da zasu kuduri niyyar farawa, domin kuwa abunda yake fara zuwa
zukatansu yayin fara harkar crypto shine, zasuyi kudi nan ba da jimawa ba, suna
tunanin cewa da kudi dan kadan za su samu miliyoyin kudade, saboda kawai sunga
wani ko wata na faca kala da kudi, wanda kuma hakan ba karamin kuskure bane.
Domin su wadannan wanda suke faca kala da kudin bakusan tayanda suka fara ba,
ba kuma kusan irin kalubalen da suka hadu dashi ba kafin su fara wanna faca
kala da kudin ba.
Kuskure na biyu da yawancin mutane keyi yayin fara kasuwancin
crypto shine, da zarar mutum yaga wani dan uwansa ko abokinsa nasamun kudi da
harkar, kawai shima sai yai kundun bala ya afka batare da ya wani nemi sani
akan harkarba. Rashin ilima akan harkar crypto bakaramin tasiri yake ba akan
mutum wajen dakileshi daga barin samun alkhairan dake cikin crypto din ba,
domin ta iyayiwuwa a dai-dai lokacin da zaka shika kasuwar yazamto cewa
farashin kasuwa kasa yakeyi awannan lokacin, kai kuma baza ka iya fahimtar
hakan ba saboda rashin ilimi, hakan zaisa kana shiga kasuwa tafarayin kasa da kai,
sai kaga mutum daga shiga ya fara da asara.
Har wayau dai na daya daga cikin kuskuren da mutane keyi
yayin fara kasuwancin crypto shine gaggawa. Dayawa daga cikin masu fara
kasuwancin nan akwai su da gaggawa, burin mutum shine yafara yau ace kuma gobe
yayi kudi, wannan tunanin shi yake hana dayawa daga cikin mutane rike coin din
na tsawon lokaci, wanda da zarar mutum yaga yadan samu wata riba ‘yar kadan sai
yai wub wa fuce daga kasuwa, shi yana ganin cewa wai yayi fita da fitarsa, daga
baya kuma in bai wasaba sai yaga wannan coin din ya ninka sau ninkin baninkin,
wanda hakan zai haifarwa da mutum da nasani.
Na daya daga cikin abubuwan da ke hana mutum samun kudi a crypro
shine, saka kudi dan kadan, babu yacce fa za ai wani yasa sama da $100, kai
kuma kasa abinda bai wuce $10 ba kuma wai kai tunanin za kusamu riba iri
dayaba, domin hausawa ma suna cewa, wai da kudi ake neman kudi. A lokacin da kasa
abinda bai fi $10 ba kasamu ribar $5 zowa $10, to da $100 kasa to fa ribar $50
zuwa $100 zakasamu. To kayi tunanin inda sama da $100 kuma kasa fa, ya ribarka
zata kasance.
Abu nakusan karshe shine, dayawa daga cikin mutane dake son
fara kasuwancin crypto akwaisu da son banza, domin zakaga mutum wai shi bazai
sa kudinsaba ya sai coin sai dai yai ta bin air-drop, in kuma ma zai siyadin
sai dai ya sai shit-coin. Malan infa kana son samun kudi to dolefa kasaki kudi
kasai abu mai karko da nagarta, domin shine in yazama wani abu gobe zai iya
baka kudi masu yawan gaske.
Bazan gama bayani naba batare da na amfaci tsoroba. Tsoro na
daya daga cikin manyan kuraruren da mutane suka kasance suna aikatawa yayin
fara kasuwancin crypto. Mutum kan iya yin shahada yafara harkar crypto, amman
inda matsalar take shine, da zarar yaga kudadensa sunfarayin kasa sai kawai yai
wub ya ciresu, saboda wai yana tsoron kar ya rasasu, wanda kuma daga bisani sai
kaga kasuwar tadawo taci gaba dayin sama, wanda da ace yana ciki da tuni yafara
samun riba. Har kullum muna fadawa mutane ga duk wanda yake son fara harkar
kasuwancin crypto, to ya fara da kudin da yasan cewa zai iya daukan asararsu,
ta yanda ko sun bata bazai wani damu ba akansu domin daman yafi karfinsu, ya
kuma fiddarai akansu, dan bama ya wani lissafi da su. Mutukar dai mutum zai yi
hakan to insha Allah ko da ace yaga kudinsa na yin kasa, ba zai wani damuba
domin daman ya sadaukar da su ne.
Wadannan sune kadan daga cikin dalilan da suka sa haryanxu
kake/kike ganin bakiyi kudi ba da harkar crypto. Muna fatan ‘yan uwa zasu
fadakantu domin sugyara, wala’alla ko suma sa samu nasu rabon a harkar crypto.
Idandai har kunji dadin wannan bayanin namu, ko kuma kunajin
cewa kun samu wani ilimi, to dan Allah kuyi kasa kadan da wannan bayanin,
zakuga contact us form sai kucike shi domin gaya mana yadda kukaji game da
wannan sakon namu, mun gode, muna fatan dai ko fatan Alkhairi ne kuyi mana, sai
munji daga gare ku.
3 Comments
ALLAH yakara basira
ReplyDeleteAllah ya qara fasaha, Kuma ya biya maka buqatarka ta Alkhairi
ReplyDeleteAmin summa Amin, muna matuqar gdy
Delete