A wannan rubutun namu na yau, za mu koyi yacce mutum zai iya yin amfani da wasu tsinkayen nuna farashi (candlesticks) wajen iya hakaito inda farashin wannan kasuwar zai yi. Shin farashin wannan kasuwar tashi zaiyi ko kuwa sauka zaiyi? In tashi zaiyi a dai-dai inane muke sa ran cewa wannan farashin zai tashi? Idan kuma sauka zaiyi a dai-dai ina muke sa ran cewa zai fara sauka din? Wannan shine abunda za mu koya  ta hanyar lazamtar wasu takaitaccun tsinkayen nuna farashi (candlesticks).

Musani cewa ko wane tsinken nuna farashi (candlestick) a kwai sakon da yake isar mana a duk lokacin da ya bayyana akasuwa, sai dai kuma a kwai wasu kebantattu da idan har suka bayyana a inda ya dace, suna bamu tabbacin cewa, acikin kaso dari, kaso saba'in wannan kasuwar tashi za tai, ko kuma sauka zatai. Kadan daga cikin wadannan tsinkayen nuna farashin (candlesticks) sune kamar haka;

i. Engulfing bar

Engulfing bar tsinkayen nuna farashi ne (candidates) guda biyu da suke bayyana a akarshen ko wace kasuwa, tsinken karshen yana fin na biyun karshen tsahi a ko wane lokaci. Idan tsinken karshen yafi na biyun karshen tsaho, shine muke kiran su da engulfing bar, bi ma'ana dai shine, tsinken karshen ya rufe tsinke na biyun karshen, ko muce tsinken karshen ya goya tsinke na biyun karshen. Misalin wadannan tsinkayen (engulfing bar) sune kamar haka


Engulfing bar yana samuwa ne a waje biyu, wato bullish engulfing bar (wanda yake nuna mana cewa wannan kasuwar sama zatayi) da kuma bearish engulfing bar (wanda yake nuna mana cewa wannan kasuwar kasa zatayi)

Bullish engulfing bar

A duk lokacin da bullish engulfing bar ya bayyana a dai-dai kan support mai karfi, train line, simple moving average, 50 or 60 Fibonacci retracement ko kuma wani waje mai mahimmancin gaske, to wannan ala mace da ke nuna mana cewa wannan farashin kasuwar tashi zaiyi, abun da yaka mace mu shine mu siya (buy) a wannan kasuwar.

Yadda bullish engulfing bar yake samuwa shine, yana samuwa ne yawanci a ko wane support, sannan kuma tsinken karshen bullish ne (nuna alamar tashin kasuwa) na biyun kuma wato gajeren bearish ne (alamar nuna faduwa a kasuwa). Misalin bullish engulfing bar


Sau da dama idan wannan alamar ta bayyana a kasuwa tana nuna mana cewa wannan farashin kasuwar tashi zaiyi abun da ya kama cemu shine mu siyi wannan kasuwar (buying). Bari muka misalin bullish engulfing bar a cikin kasuwa.



Bearish engulfing bar

Shi kuma wannan kishiyar bullish engulfing bar ne, yawanci yana samuwa ne a duk wani resistance mai karfi ko simple moving average ko kuma duk wata alama da ka iya nuna cewa tafiyar kasuwa ka iya canzawa.


Cikakken bayani akan engulfing bar

Yadda bearish engulfing bar ke samuwa shine, tsinken karshen bearish ne (alamar faduwar farashi) shi kuma na biyun karshen bullish ne (alamar tashin farashin), misalin bearish engulfing bar shine kamar haka



A mafiya yawan lokuta bearish engulfing bar na nuna mana cewa farashin wannan kasuwar faduwa zaiyi, abun da yaka mace mu shine selling wato siyarwa. Misalin bearish engulfing bar a cikin kasuwa.



ii. Harami

Harimi suma wasu tsinkaye ne guda biyu da suke bayyana a karshen kasuwa, kamar dai engulfing bar suke, sai dai su Harami dogon tsinken ne yake zuwa a na biyun karshen sai kuma kajeren ya zo a na karshen, sabanin engulfing bar. Misalin Harami 



Sau da dama idan Harami candlestick ya samu a support ko resistance, wannan na nuna mana cewa farashin wannan kasuwar tashi zai yi, ko kuma sauka sai yi.

Kamar yanda yaka sance cewa akwai bullish engulfing bar da bearish engulfing bar, haka shima Harami yakasance yana da bullish Harami da kuma bearish Harami.

Bullish Harami

A duk lokacin da Harami candlesticks suka bayyana a dai-dai support mukan kirasu da bullish Harami badan komai ba sai dan wannan alama ce da ke nuna cewa wannan kasuwar tashi zatai, wanda abun da yaka mace mu a dai-dai wannan lokacin shine mu siyi wannan kasuwar (buying). Misalin bullish Harami shine;



Bearish Harami

Mukan samu bearish Harami candlesticks ne a dai-dai residence, sannan kuma tsinken karshen zai kasance bearish ne, shi kuma na biyun karshen bullish ne, a duk lokacin da muka ga wannan alamar, to alama ce da ke nuna cewa farashin wannan kasuwar faduwa zai yi, abun da ya kama cemu a wannan lokacin shine siyarwa (selling). Misalin bearish Harami candlesticks;



Misalin bullish Harami da kuma bearish Harami a kasuwa shine kamar wannan hot on na kasa


Bayani akan Harami pattern cikin video


iii. Doji pattern
Domin sanin yadda Doji pattern yake tare kuma da wasu patterns din ku kalli wannan video na kasa


iv) Price action
Domin ganin cikakken bayani akan sauran tsinkayen nuna farashi sai ku kalli wadannan videos din na kasa





Wannan sune kadan daga cikin tsinkayen nuna farashin da muke da su kenan, domin iya gano inda farashin kasuwa ka iya yi agaba.
A karatun nagaba zamu shiga bayani akan Technical analysis.