TARIHIN TSINKAYEN NUNA FARASHI (CANDLESTICKS)


Tsinkayen nuna farashi (candlesticks) na daya daga cikin mafiya dadewar ababen tarihi na yammacin duniya. Mutanen kasar japanese sun kasance suna amfani da wadannan tsunkayen nuna farashin (candlesticks) sama da karni goma shabakwai da suka wuce, wanda kuma yankin turawa sun fara amfani da wadannan tsinkayen nuna farashin ne (candlesticks) bayan  karni na goma shatara.
Ashekara 1654 mutanen kasar japan sun kasance suna siye da siyarwar shinkafa tahanyar misayar ta da gold, silva ko kuma wani abu mai daraja, wanda hakan ya karade dukkan nahiyar, har yazamto cewa cinikayyar shinkafa yafi matuqar muhimmanci akan sauran cinikayyar da ake kullawa da kudi.
Munehisa Homma, daya daga cikin mafiya shaharar kasuwancin shinkafa a japan, an haife shine a farkon karni na shabakwai, wanda yazamto daya daga cikin mutanen farko-farko da suke iya gano loacin hawa da saukar farashin wannan kasuwancin na shinkafa.
Yayi kokari wajen yin amfani da tunanin mutane wajen gano lokacin da farashin wannan shinkafar ke ta shi da kuma sauka, kuma yayi nasara, domin ya fahimci cewa tsinkayen nuna farashi (candlestics) na taka mahimmiyar rawa wajen iya hakaito abunda mutane ke tunani a game da kasuwar.
A dalilin wadannan tsinkayen ne yazamana cewa Munehisa Homma, na iya hakaito yadda farashin kasuwar zai iya kasan cewa a gaba, duba da irin ra'ayoyin mutane da kuma irin abunda suke tunani a game da kasuwar.
Munehisa Homma ya zama abun girmamawa a wannan lokacin, saboda samun nasarar da yai wajen yin amfani da tsinkayen nuna farashi (candlesticks) dan gano yanayin da kasuwa ka iya kasan cewa a gaba.
Mutanen kasar japanese sun kai makura wajen ganin sun bar wannan al'amarin ya tsaya a iya tsakanin su, ta hanyar boyewa mutanen da ke rayiwa a yammacin duniya, har kusan karni na ashirn suka kai batare da sunbar wasu sun san wannan tsarin nasu ba na tsinkayen nuna farashi (candlesticks). sai bayan bayyanar manyan bankuna da manyan ma'aikatu a duniya sannan mutane dake sauran bangarorin duniya suka fara fahimtar wancan tsarin na tsinkayen nuna farashi (candlesticks).
Domin a wannan lokacin ne kafafen sada zumunta na yanar gizo-gizo suka yawaita, saboda samun yalwa na yawan na'ura mai kwakwalwa (computers).
A karshen karni na shatara dayawa daga cikin masu hasashen farashin kasuwa dake yammacin duniya, suka fara sha'awar amfani da tsarin tsinkayen nuna farashi (candlesticks). Michael Feeny, daya daga cikin shuwagabannin london a wancan zamanin, ya fara amfani da tsinkayen nuna farashi (candlestucks) a kasuwancin sa na yau da kullum, sannan kuma yafara kogarin nusar da manya-manyan farfesoshin da ke londan fa'idar amfani da wadannan tsinkayen nuna farashin (candlesticks).
A December 1989, wani babban masani agame da fahimtar yaren tsinkayen nuna farashi (candlesticks) wato Steve Nison, ya wallafa wasu takaddu da ke dauke da hotunan tsinkayen nuna farashi (candlestick), tare kuma da yin cikakken bayani agame da duk wani tsinken nuna farashin (candlestick) da kuma irin sakon da yake kunshe da shi, hakan har ya kai shi ga wallafa littafi agame da tsinkayen nuna farashi (candlesticks). Muna matukar godiya ga Messrs Feeny da kuma Nison.
Tundaga wannan lokacin amfani da tsinkayen nuna farashi (candlesticks) ya kara samun karbuwa a sassan duniya daban-daban, wanda ayanzu haka wannan tsarin na amfani da tsarin yaren tsinkayen nuna farashi (candlesticks), shine tsari mafi girma da mutane ke amfani da shi wajen iya fahimtar yanayin hawa da saukar farashin kasuwar forex.
Meyasa tsinkayen nuna farashi (candlesticks) ke da amfani yayin gudanar da kasuwancin forex?
-Tsinkayen nuna farashi (candlesticks) na da matukar muhimmaci agare mu yayin son sanin halin da kasuwa ka iya kasancewa a gaba, domin kasantuwar wadannan tsinkayen nuna farashin ne (candlesticks) ke sanar damu halin da kasuwa ke ciki, ko ka iya kasan cewa agaba.

Kalli vidiyon nan domin ganin cikakken bayani
Ta hanyar amfani da wadannan tsinkayen nuna farashin (candlesticks) zamu iya fahimtar a daidai ina farashin wannan kasuwar  yafara, inane mafi qololuwar farashin nan zaije sannan kuma inane mafi kankantar farashin da wannan kasuwar zata iya komawa, wanda ta hakan ne zamu iya kintatar yanayin da kasuwar zata iya kasancewa agaba.
-Tsinkayen nuna farashi (candlesticks) tabbatattun abubuwa ne, ta yacce zamu iya dogara da su wajen fahimtar yanayin kasuwa, ko kuma muhada wadannan tsinkayen nuna farashin (candlesticks) da wasu hanyoyin da suka tabbata wajen gano inda farashin kasuwa ya dosa.
Munehisa Homma cewa yai, ya kasance yana hada tsinkayen nan tare da wasu alamomin na daban da suke iya bada labarin yacce yanayin kasuwa zai iya kasantuwa agaba dan gano lokacin da yaka mata ace ya shiga ko fita a kasuwa, wanda insha Allah zamuga wadannan abubuwan a gaba cikin wannan littafin.
-Dayawan mutane sun kasance kwadayayyu ne agame da batun kudi, son zuciya da kuma tsoron asara na daya daga cikin dabi'un wasu mutanen. Amfani da tsinkayen nuna farashi (candlesticks) ka iya zama madogara wajen iya fahimtar yadda dayawa da ga cikin mutane ke shiga da fita a wannan kasuwa ta forex.
-Tsinkayen nuna farashi (candlesticks) ka iya zamar mana wata alama da zata ringa nuna mana dai-dai inda yakamata ace mushiga kasuwa ko mufita daga wannan kasuwar.
-Kwararru da manyan masu kudi, kana kuma da manyan bankuna sun kasance ma su amfani da wadannan tsinkayen nuna farashin (candlesticks) wajen shigar su da fitar su a kasuwa, wanda irin manyan kudaden da wadannan manyan mutanen ke sawa akasuwa ne ke iya nuna inda farashin da kasuwa zatai. Yin amfani da tsinkayen nuna farashi (candlesticks) zai bamu damar cin moriyar shiga da kuma fita a kasuwar tare da wadannan manyan mutanen, wanda hakan ba karamar nasara bace a tare da mu ba.
Kusani rashin fahimtar yanda wadannan manyan mutane ke gabatar da kasuwancin su na iya jawa mutum babbar asara, domin kuwa farashin kasuwar na motsawa ne da shigarsu ko fitarsu. Hanya daya mafi girwa wajen fahimtar lokutan da wadannan manyan gwasaken ke shige da ficensu a kasuwa itace hanyar amfani da tsinkayen nuna farashi (candlesticks).
Wadannann sune kadan daka cikin dalilan da za su iya samu yin amfani da wadannan tsinkayen nuna farashin (candlesticks) domin samun damar cin ribar wannan kasuwancin.
MENENE TSINKAYEN NUNA FARASHI (CANDLESTICKS)
Tsinkayen nuna farashi (candlesticks) na samuwa ne daga lokacin da farashin kasuwa ya bude izuwa matakin da wannan farashin kasuwar zai iya kaiwa, sannan kuma ya rufe bacin ya taba kololuwar inda zai sauka.


Wadannan tsinkayen nuna farashin (candlesticks) sun rabu gida biyu. Idan ya zamana cewa farkon inda fara shin wannan tsinken ya fara, kasa yake da inda farashin nasa ya rufe yake, to wannan tsinken na nuna cewa farashin kasuwar tashi sama yake. Ana yiwa wannan tsinke lakabi da bullish a yaren turanci kenan.
Idan kuma ya zamana cewa inda fara shin wannan tsinken ya fara, sama yake da inda fara shin nasa ya rufe, to wannan tsinken na nuna cewa fara shin wannan kasuwar kasa yakeyi a wannan lokacin. Ana yiwa wannan tsinken lakabi da bearish a turance shi ma.
Tsinkayen sunkasance na da kaloli mabambamta. Sau da dama mutane na amfani da koriyar kala ko farar kala wajen gane tsinken farashin da ke nunin farashi izuwa sama (bullish), me nuna kuma farashi nayin kasa (bearish) sukanyi amfani da jar kala ko baka. Sai dai kalar bawai itace mafi mahimmancin ba, face kawai sanin mabudar wannan tsinken da kuma marufarsa.
Sau da dama wadannan tsinkayen nuna farashin (candlesticks) na fitar da wani siririn layi a saman su da kuma kasan su, kamar dai yadda muka gani a hoton baya. Wannan siririn layin na saman su na nuna mana mafi kololuwar fashin da suka taba ne a lokacin da farashin ke tashi, haka zalika shima wannan siririn layin na kasan su na nuna mana mafi kankantar farashin da suka tafa yayin da farashin ke sauka. kakkauran jikin da ke tsakanin siririn layin da ke saman tsinen da kasan sa, shine ainahin gangan jikin tsinken nuna farashin (candlesticks).
SIFFOFIN TSINKAYENN NUNA FARASHI (CANDLESTICS)
Tsinkayen nuna farashi (candlesticks) na da siffofi mabamban ta, akan samu dogaye ko gajeru, kamar dai a wannan hoton na kasa.
Dogon tsinken nuna farashi (candlestick) na nuna cewa ana hada-hada a wannan kasuwar, ya danganta da wannene daga cikin tsinkayen ya bude. in yazamana cewa inda farashin wannan tsinken yafara, kasa yake da inda farashin ya rufe yake, sannan ya zamana cewa tsinke dogo ne, to wannan tsinken na nuna cewa akwai masu siyan wannan kadarar da yawa a wannan lokacin, shiyasa farashi ke tashi.
Idan kuma ya zamana cewa inda farashin wannan tsinken yafara sama yake da inda farashin nasa ya rufe, to wannan tsinken na bamu labarin cewa akwai masu siyarwa da yawa a wannan kasuwar, shi yasa farashi kasuwar keyin kasa.
Gajeren tsinken nuna farashi (candlestick) kuma na nuna cewa babu wasu mutane da yawa a kasuwar da ke siya ko siyar wa.
JELAR TSINKEN NUNA FARASHI (CANDLESTICK)
Jelar tsinken nuna farashi itace wannan dan siririn layin da ke bayyana a saman tsinken nuna farashi (candlestick) ko kasan sa.

Jelar tsinken nuna farashi (candlestick) na da matukar mahimmanci agare mu, yayin gano halin da kasuwa ke ciki. idan ya zamana cewa an samu tsinken nuna farashin (candlestick) da jelar sa ta sama tafi tsahon ainahin jikin sa, to wannan na nuna mama cewa lokafin da farashin ya fara sama, an samu masu siyarwa da yawa sun shigo wannan kasuwar, wanda hakan yasa suka fara karya farashin wannan kasuwar.
Idan kuma ya zamana cewa jelar tsinken nuna farashin (candlestick) tafi tsaho ta kasa, hakan na nuna mana cewa da fari farashin kasuwar kasa yakeyi daga bisani kuma sai masu siya da yawa suka shigo wannan kasuwar, wanda hakan ya fara haifara ta tashin farashi a kasuwar
Wannan shine dan takaitaccen bayani a game da Tsinkayen nuna farashi (candlesticks). muna fatan 'yan uwa da abokan arziqi sun dan amfana da wannan dan takaitaccen bayanin namu. A rubutunmu nagaba insha Allah zamu zo muku da bayani price action (wato fahimtar inda farashin kasuwa zaiyi ta hanyar amfani da tsinkayen nuna farashi). Mungode
Akarshe nake cewa dai har kullun ni ne naku Abdurrahman Auwal Ahmad me son cigaban ku, Assalamu'alaikum warahmatullahi wa baraka tuhu.