Kamar yadda bayani yaga bata abaya game da major currencies da kuma minor currencies, a wannan rubutun namu kuma zamuyi bayani akan base currency da kuma quote currency.
BASE CURRENCY:- Base currencies sune ne wadannan kudaden da suke zuwa a farko yayin rubuta harufan da ke nuna kudi. Misali GBPUSD, anan GBP shine base currency din mu, domin shine yazo a farko. Kamar EURUSD, anan kuma EUR shine base currency din mu, domin shine yazo a farko. Kamar USDCAD, anan kuma kunga USD itace base currency domin itace tazo a farko.
QUOTE CURRENCY:- Quote currencies su kuma sune suke zuwa a na biyu, misali EURUSD, USD anan shine quote currency din. USDCAD, CAD shine quote currency din mu anan domin shine yazo a na biyu.
Kullum Base currency din mu shine yafi tsada akan quote currency. Euro yafi dalar Amurka tsada shiyasa aka rubutasu kamar haka EURUSD. Dalar amurka kuma tafi dalar Canada tsada shiyasa aka rubutasu kamar haka USDCAD.
SPREAD:- spread shine ribar da broker din da mutum yake amfani da shi yake samu a duk wani trading da mutum ya shiga.
Kamar yadda muka sani cewa, kasuwancin forex anfarashi ne tsakanin kasa da kasa ta yacce manyan bankunan duniya ne ke iya cin wannan kasuwar da kuma manyan masu kudin duniya. Ni da Kai da jarin kudin mu bai wuce wasu kananun daloliba, baza mu iya shiga kasuwar forex kai tsaye ba domin cin kasuwa, hakan yasa wadan nan brokers din suka bamu dama kan cewa musaka kudaden mu a platforms dinsu ta yadda zasu hada kudaden namu waje daya yanda in yawan kudin namu yakai mushiga kasuwar sai mushiga muyi kasuwancin namu, aman duk lokacin da muka shiga kasuwar a ta dalilin su akwai wani dan abu da suke samu a kudin mu, wannan abun shine ake kiransa da spread a forex.
A duk lokacin da mutum yashiga kasuwar forex zai ka layin da yake nuna farashi guda biyu ne, kore da kuma ja, to dan abunda yake tsakanin koren layin da kuma jan layin shine spread din. Ga misalinan a wannan hoton na kasa
PIPS:- Pips lissafine na ribar da mutum zai iya samu ko kuma kudin da mutum zai iya rasawa a duk tafiyar da kasuwa keyi. Yana da matukar muhimmanci ace mutum ya iya lissafa tafiyar pips a duk wani trading dai zai shiga, domin tahakan ne mutum zai iya sanin ribar da zai samu a duk wani trading din da yashiga ko kuma kudin da zai iya rasawa a duk wani trading da zai shiga.
Domin ganin cikakken bayani akan yadda ake lissafa pips sai ku kalli wannan video na kasa.
Idan mutum yashiga da 0.01 to a duk pips 10 zai samu ribar $1 ko kuma yai asarar $1, ya danganta da inda farashin kasuwa yayi. Idan kuma da 0.02 mutum ya shiga zai samu riba/faduwa ta $2 a duk pips 10. Riba/Faduwar $3 a duk pips 10 idan da 0.03 mutum ya shiga, haka dai har zuwa 0.09 mutum zai samu riba/faduwa ta $9 a duk pips 10.
Idan kuma mutum yashiga da 0.1 a duk pip 1 zai samu ribar $1 ko yai asarar $1, yadanganta da yandda kasuwar take ta fiya. Idan kuma mutum ya shiga da 1 to fa a duk pip daya zai iya samun riba ko asarar $10.
Idan mutum bai gane wannan lissafin ba, to ya kalli wancan vidiyon na sama domin ganin a bun a zahiri.
Wannan shine dan takaitaccen bayani a game da base currency, quote currency, spread da kuma lissafin pips. muna fatan 'yan uwa da abokan arziqi sun dan amfana da wannan dan takaitaccen bayanin namu. A rubutunmu nagaba zamu zo muku da bayani akan tsinken nuna farashi (candlestick). Mungode
Akarshe nake cewa dai har kullun ni ne naku Abdurrahman Auwal Ahman me son cigaban ku, Assalamu'alaikum warahmatullahi wa baraka tuhu
.jpeg)

0 Comments