<\head>


 


Akwai dubbannin hanyoyi da mutum zai iya jawo mutane izuwa sabon shafinsa (website), kadan daga cikin su sune wadannan guda biyar din da zamuyi Magana akansu

1. Search Engine Optimization (SEO)

Wannan wani injine da zai bawa shafinka dama wajen idan mutum yashiga internet ya rubuta tambayarsa, amsarka ta zamo daga farko farko, ta yadda in har kasa bayanai masu amfani zasu iya jan ra’ayin mai karatu yafara shika naka shafin. Hakan zai taimakama wajen jawo mutane izuwa shafinka.

2. Amsa tambayoyi a cikin groups

Idan har yazamanto cewa kana shiga cikin groups na social media dake dauka da mutanen da ke sha’awar irin kasuwancika kana bada amsa, hakan zai sa mutane sufara saninka harma su fara biyoka shafinka domin samun Karin bayani game da matsalolinsu.

3. Biyan face-book kudi don tallatama shafinka

Face-book na bawa mutane dama wajen ganin suntallata musu shafinsu akan kudi dankadan domin su samu karbuwa a idon jama. Hikimar anan shine, tunda har akwai miliyoyin mutane a face-book, to akwai yiwuwar in har face-book suka tallata maka shafinka to za kasamu masu ziyartarsa akai-akai

4. Rubutu a shafin wasu

Indai har zaka ringa ziyartar wasu shafukan makamantan nakan kana danyin jawabi a comment section din su dangane da matsalar mutane, to tabbas hakan zai tai maka wajen jawoma mutane naka shafin

5. Abubuwa masu muhimmanci

Mutukar dai zakaringa saka abubuwa masu muhimmanci a shafinka, hakan bakaramin taimakamaka zai ba, domin muddin yazamto cewa baka wani sa abu masu amfani to duk wanda yazo shafinnaka, bazai kara dawowaba.