<\head>


 



Akwai dalilai dayawa da zasu iya sa mutum ya fara kasuwannancin yanar gizo-gizo (online business), amman ga guda biyar nan daga ciki wadanda muke tunanin cewa zasu iya sa mutum ya fara kasuwancin yanar gizo-gizo (online business).

1. Baka bukatar ko sisi yayin farawa

Wani abun burgewa game da kasuwancin yanar gizo-gizo (online business) shine, zaka iya fa rashi batare da kana da sisi ba, mutukar dai zaka iya siyan datar da zakai amfani da ita, sabanin kasuwancin zahiri da dole sai ka mallaki jari. Kadan daga cikin kasuwancin yanar gizo-gizon (online business) da mutum zai iya farawa batare da ya sanya ko sisi ba sune kamar haka; Affiliate marketing, selling e-book online, Google ads dadai sauransu. Wannan na daya daga cikin dalilan da zai iya sa mutum yafara kasuwancin yanar gizo-gizo (online business).

2. Saukin farawa

Kasuwancin yanar gizo-gizo (online business) saukin farawa ne dashi, domin baka bukatar kama haya ko mallakar wani waje yayin farawa. Baka bukatar wasu ma’aikata da za suringa kulamma da wannan kasuwancin naka, mutukar dai kana da computer ko kuma wayar hannu, Magana takare, domin kawai farawa zakai mutukar dai kana da ilimi akan hakan.

3. Cikakken iko

Kamar yadda muka sani cewa lokacin da yazamto cewa kana aiki a karkashin wani to yazamema dole fa kai hakuri, domin bazaka taba samun yadda kake so ba. A mafiya yawan lokuta masu aiki a qarkashin wasu na iya fuskantar wulakanci da kuma kaskanci. Amman shi kasuwancin yanar gizo-gizo(online business) mallakin kane, to kunga kenan mutum na da cikakken iko da abunsa, sai yanda yaga dama zaiyi da abunsa, sabanin ace akarkashin wani kake aiki.

4. zaka iya yinsa ako ina kake

Wani abun burgewa da kasuwancin yanar gizo-gizo (online business) shine, zaka iya farashi ako ina, misali mutum zai iya farashima daga gidansa. Idan dalili yasa mutum ya bar wannan gidan yakoma wani wajen, misali ace yabar garin to kaitsaye zaici gaba da kasuwancinsa batare da yayi asarar abokan kasuwancinsaba, sabanin kasuwancin zahiri da in har dalili yasa kabar wajen kasuwancinka kakoma wani wajen, to dolefa kasake kokarin kafa wannan kasuwancin awajen.

5. Gwaggwabar riba

Mutukar dai mutum zai tsaya yai kasuwancin nan nasa yadda yakamata to tabbas babu makawa zai samu gwaggwabar ribar da bai taba tunani ba, kawai abunda ake bukata shine kabawa kasuwancin naka lokaci yayin ginashi. Wani abun burgewama shine, ko dama ace kabawa kasuwancin naka lokaci mai yawa, hakan bazai hanaka gudanar da al’amuranka ba na yau da kullu.

Wadannan sune kadan daka cikin dalilan da muke tunanin cewa zasu iya sa mutum ya fara kasuwancin yanar gizo-gizo (online business). Muna fatan kun dan samu wani haske da kuma Karin ilimi game da kasuwancin yanar gizo-gizo. Kukasance da a-mangroup.blogspot.com domin koyon yadda zaku fara samunnan naku kudaden, mungoe.