<\head>


 



Akwai hanyoyin samun kudi da yawa bayan kasuwancin yanar gizo-gizo (online business) masu saukin gaske, amman meyasa sai kasuwan yanar gizo-gozo (online business). Wannan shine abuna a-mangroup.blogspot.com keson yin bayani akai insha Allah.

Sanin kanmu ne cewa hanyoyin samun kudi a wannan zamanin sun sha banban dana zamin baya, saboda samun canjin yanayi da mukeyi da kuma irin cigaban da duniya ke kara samu a duk kwanan duniy.

A da, mafi yawancin lokuta mutane basu cika rasa aikin yi ba, amman kuwa yanxu labarin ba haka yake ba musammanma a gwamnatance, domin kuwa mafi yawancin al’ummarmu zaman banza sukeyi. Abun tambaya anan shune, shin ka/kin taba zama dai-dai da lokaci guda domin yin tunani akan dalilin hakan kuwa? Shin kuntaba tunani akan ya yakamata ace an bulluwa wannan matsalar kuwa? Wannan shine abunda a-mangroup.blogspot.com yake son yin bayani akai.

Sanin kankune cewa yanzu muna wani zamani ne da ke cike da ilimin kimiyya da fasaha (science & technology). A wannan zamanin, duk wani aiki da yakasance dan adam nayinsa to wannan fasahar ta kimiyya itama na iya yinsa, ta hanyra samar da injinan da zasu gudanar da wannan aikin. Abun burgewarma shine, wadannan injinan na iya yin aiki fiyema da yanda dan adam zaiyi.

A wannan zamanin da muke, duniya ta fara fahimtar cewa aiki da irin wadannan injinan da kimiyya da fasaha suka kawo mana, yafi aiki da dan adam, badan komai ba sai dan aikin da mashin zaima a awa daya to in mutum ne, zai iya kwashe wunin baki daya kafin gama aikin. Wannan dalilin dama wasunsu ne sukasa duniya tafara karkata kan amfani da irin wadannan injinan akan aiki da bil’adama.

Bari muga misalai guda biyu kwarara da zasu iya tabbatar mana da cewa kimiyya (technology) na barazana ga ayyukanmu.

1.     A lokutan baya kafin zuwan kimiyya (technology) idan kana da dan uwa a wani garin kuma kanason sanar da shi wani sako, tofa sai dai karubuta wasika sannan ka kai ofishin jakadanci na wasiku domin su aika maka da ita izuwa ga dan uwan naka, wanda hakan yakan dan dauki lokaci kafin sakonka ya isa indan ka turashin. Amman yanzu zuwan wahar hannu wato salula ya saukaka komai, domin kafin kiftawa da bisimilla yanxu zaka iya tura sakonka duk inda kakeso afadin duniya, kuma da kudi dankadan. Bayan hakama harmuryar mutum zaka iya ji batare da kuna tare ba. Kai bama wannan ba yanxu harganin mutum zaka iya yi kugana batare da kuma kuna gari daya ba.Wannan sabuwar fasahar ta sa dole aka rufe ofisoshin jakadancin wasiku, domin ba’a da bukatarsu.

2.     Misali na biyu shine lokacin da baki yazo mana, Idan kaje cirar kudi a banki akalla ba akasaraba ka tarar da masu bada kudin guda biyar, ko wannensu na bada kudi, amman yanxu saboda zuwan ATM yasa dole banki basu da buqatar wadannan masu bada kudin, to ko mai yasa hakan? Saboda wadannan dalilan kamar haka:

i.                    Nafarko shine, ATM ba’a yi masa salari, sukuwa wadannan mutanen dolene banki ya biyasu kudin duk wani aiki da sukai masa.

ii.                  Na biyu, ATM 24 awa yake aiki wanda su kuma wadannan mutanen baifi aikin awa shabiyu sukeyi ba akullum.

iii.                Dan adam larula zata iya kamashi a dai-dai lokacin da yake aikin sa kamar zuwa ga bandaki da makamantansu, amman shi ATM bashi da wadannan buqatuwar.

Wadannan dalilan da ma wasunsu ne za su sa banki surabu da wadannan ma’aikatan nasu surungumi ATM, bad an komai ba sai dan garesu samun sauki ne hakan.Baya ga wadannan misalan, idan mukai duba izuwa bangaren tsaro, lafiya da kuma noma zamuga cewa wannan fasahar tana kirkiro mana sababbin mashina da zasu iya yin aiki fiye da yadda dan adam ma yakeyin aikin.

Har wayau dai wannan fasahar ta kimiyya (technology) bata tsaya iya nan ba, domin idan mukai duba izuwa bangaren ilimi zamuka cewa tana barazana izuwa aiyyukan mutane, domun yanxu daga gida ma zaka iya yin karatunka ka kammala harma a turoma sakamakonka. Kusanifa muddin dai akacigaba da tafiya ahaka, akwai yiwuwar cewa, kamar yadda ma’aikatan jakadancin wasiku suka rasa ayyukansu a dalilin wannan kimiyyar, to haka malaman makaranta, jami’an lafiya da kuma jami’an tsaro suma zasu rasa nasu.

Idan har kun fahimceni da kyau, kenan zaku iya fahimtar cewa  akwai yiwuwar wannan fasahar (technology) zata iya mamaye duk wani aiki da mutum yake tunanin zai iyayinsa domin samun kudi. To inko hakane, ina mafita?

Hausawa suna wata Karin Magana wai “ta inda akabi aka hau, tanan ake bi a sakko” abunda nake  nifi anan shine, yadda wannan fasahar take raba jama’a da ayyukansu to kuma tana zuwar musu da damarmaki da yawa wacce zasu iya yin amfani da ita domin samun kudin shiga. Ya ishemu izina akan manya-manyan masu kudin duniya. Ko da kuwa ace ba dukkansune suke kasuwancin yanar gizo-gizo ba amman mafiya yawa daga cikin su wannan fasaharce ta daukaka matsayin su a duniya.

Wannan shine dalilin dayasa mukace kasuwancin yanar gizo-gizo (online business) shine hanya mafi sauki da in mutum yayi shi yanda yadace zai iya canza rayiwarsa daga matakin da yake izuwa nagaba. Amman ta iya yiwuwa wani yace shi ai baisan tayadda zai faraba. Kar ka/ki damu dan uwa/’yar wa, ku dai ku kasance da mu awannan shafin namu na a-mangroup.blogspot.com  domin koyon kasuwancin yanar gizo-gizo (online business). Daman wannan shafin anbudeshine domin koyawa ‘yan uwa da kuma abokan arziki yanda zasuringa samun kudi a online ne.

Idan harkuji dadin wannan fadakarwar, ko kuma kunajin cewa kunsamu wani ilimi, to dannan Allah kuyi  kasa kadan zakuga contact us, sai kusanar damu ra’ayinku. Muna fatan zakuyimana koda fatan alkhairine. Mungode, a-mangroup.blogspot.com nakune.